Tsohon shugaban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya wato tsohon VC na ABU da shugaban sashen kuɗi na jami’ar wato Bursar, Farfesa Ibrahim Garba, da Ibrahim Shehu Usman sun gurfanar a gaban mai shari’a A.A Bello na babbar kotun jihar Kaduna bisa tuhume-tuhume takwas da suka hada da sata da kuma karkatar da kuɗaɗe sama da Naira biliyan ɗaya.
Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon kasa, (EFCC) ce ta jagoranci gurfanar da waɗabda ake zargi.
KU KUMA KARANTA:EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan Kaduna a kotu
Shari’ar dai ya biyo bayan bincike na tsanaki na tsawon watanni da wata kotu ta shigar inda ake zargin mutanen biyu da karkatar da kuɗaɗen da aka tanada don gyaran zauren taro na Kongo a Zariya.
Binciken ya tabbatar da cewa wadanda ake tuhumar sun sace sama da Naira biliyan ɗaya daga asusun ajiyar ma’ikatar tare da karkatar da su zuwa asusu na ƙashin kansu.