No menu items!

Sample Page Title

Date:

Gwamnatin Najeriya ta gurfanar da kamfanin Binance da manyan jagoririnsa biyu; Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla da ya tsere, a gaban kotu.

An gurfanar da Tigran Gambaryan a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ranar Alhamis ƙarƙashin mai shari’a Emeka Nwite.

Tigran Gambaryan ya je kotun da misalin ƙarfe 9:15 na safiyar Alhamis, amma abokin aikinsa Anjarwalla bai zo ba sabon an ce ya gudu daga ƙasar.

Har yanzu kotunan na hutun Easter amma bayanai sun ce alƙalin kotun bai je hutun ba saboda ya saurari wannan ƙara mai matuƙar muhimmanci.

Ana tuhumar mutanen biyu da laifuka biyar na halatta kuɗaɗen haramun da gudanar da kasuwanci a Najeriya ba tare da lasisi ba.

A watan jiya ne jami’an tsaron Najeriya suka tsare Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla.

Shugabannin Binance ɗin sun je Najeriya ne bayan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na rufe manhajar.

An tsare shugabannin na Binance ne saboda sun kasa ba da gamsassun bayanai kan yadda manhajar take hada-hadar kuɗi a Najeriya.

A wancan lokacin, wata majiya a fadar shugaban Najeriya ta tabbatar wa TRT Afrika cewa manyan batutuwa uku ne suka damu gwamnatin ƙasar kan hada-hadar Binance a ƙasar.

Na ɗaya, kamfanın bai yi rajista da hukumomin ƙasar ba, sannan gwamnati ba ta samun haraji daga ɗimbin ribar da Binance ke samu daga hada-hadar da yake yi a ƙasar, matakin da ke yin illa ga tattalin arzikinta.

Na biyu, babu gamsassun bayanai kan adadin ƴan Najeriya da ke hulɗa da Binance da kuma yawan kuɗin da ake hada-hadar su.

Na uku, gwamnatin Najeriya na zargi cewa masu aikata laifukan da suka shafi harkokin kuɗi da masu neman kuɗin fansa suna amfani da manhajar wajen musayar kuɗaɗe ba tare da wata kafa ta iya bibiyarsu don gano abubuwan da suke yi ba.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...