An gudanar da addu’ar roƙon ruwa a fadar Sarkin Fika da ke Potiskum

0
429

Daga Ibraheem El-Tafseer

A safiyar ranar Laraba, 1 ga watan Muharram na sabuwar shekarar Musulunci ta 1445, wanda ya yi daidai da 19 ga watan Yuli, 2023 aka gudanar da addu’ar roƙon ruwa, a babban masallacin jumu’a na ƙofar fadar mai martaba Sarkin Fika kuma shugaban Sarakunan jihar Yobe, Alhaji Dakta Muhammad Abali Ibn Muhammad Idriss da ke garin Potiskum.

Mai martaba Sarkin, a farkon nan ne ya gayyaci al’ummar musulmi domin gudanar da addu’o’i na musamman akan rashin ruwan sama da ake fama da shi, wanda hakan ya yi sanadiyyar ƙonewar amfanin gona, wasu gonakin kuma tuni har sun bushe.

KU KUMA KARANTA: Ƙarancin ruwan sama: Shehun Borno ya ce a yi addu’a

Babban limamin Masallacin jumu’a na fadar Sarkin Fika, Goni Laminu Goni Babaji ne ya jagoranci addu’o’in, inda manyan Malamai da Alarammomi da kuma al’ummar gari da dama duk sun halarta. An yi saukar Alqur’ani sau uku, sannan an gudanar da addu’o’i na musamman da fatan Allah ya ba da ruwa mai albarka da Damina mai albarka. Sannan an yi addu’o’in zaman lafiya ga ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply