An gargaɗi ’yan acaɓa kan ɗaukar fasinjoji 2 da daddare a Gombe

0
182

Kwamishinan ’yan sandan jihar Gombe, CP Hayatu Usman, ya gargaɗi ’yan acaɓan da ke watsi da shawarwarin da ake ba su na kaucewa ɗaukar fasinja biyu ko uku suna shiga lungu da daddare, inda galibi a sanadiyar haka suke faɗa wa tarkon masu kwacen babura.

Kwamishina Hayatu ya yi gargaɗin ne a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa, yana mai cewa an fi samu ta’adar kwacen baburan ’yan acaba da daddare musamman ga masu ɗaukar fasinja fiye da ɗaya.

Ya ce “an ja musu kunne, an musu gargaɗi kan haka domin kauwace shiga tarkon ɓata-garin amma ba su ɗaukar shawara.

Ya bayyana cewa galibi wannan matsalar tana faruwa ne a bayan gari a yankin Akko da ke daura da unguwannin Wuro biriji da Gona.

A cewarsa, zai yi zama na musamman da mutanen unguwannin kamar yadda suka nema domin samar da mafita.

KU KUMA KARANTA: Wani ɗan banga a jihar Neja, ya kashe ɗan achaɓa, ya sace babur ɗinsa

CP Hayatu Usman ya ce zai ja hankalin al’ummar yankin domin a haɗa ƙarfi da ƙarfe don ganin an shawo kan matsalar kwacen babura.

Ya bayyana fatansa na samun mafita da zarar an tattauna da mutanen unguwannin domin ɗaukar ƙwararan matakai da za su magance matsalar baƙi ɗaya.

Ya ci gaba da cewa, yana so wannan matsala ta ƙwacen babura ta zama tarihi saboda ya samu abin da zai yi alfahari a nan gaba.

Ya ce duk da kasancewarsa sabon Kwamishina ’yan sandan Jihar Gombe, yana da masaniyar yadda al’amura ke gudana saboda kafin yanzu shi ne Muƙaddashin Kwamishina ’Yan sanda mai kula da ɓangaren ayyuka ’yan sanda.

A cewarsa, yana da gogewar da zai kawo kyakkyawan shiri kan samar wa matasa mafita a rayuwa wajen samar musu sana’oin hannu wasu kuma a mayar da su makaranta domin da yawa suna zama bata gari ne saboda rashin aikin yi wanda a doka hakan ba hujja ba ne.

Ya yi ƙira ga sauran jami’an tsaro da su bai wa ’yan sanda haɗin kai wajen ganin sun haɗu sun gudanar da aikin su gaba ɗaya.

Kazalika, ya jinjina wa ’yan banga da mafarauta da suke aiki tare da jami’an tsaro ba dare ba rana wajen shiga daji domin daƙile aika-aikar ’yan ta’adda da ɓarayi da masu satar mutane domin karbar kudin fansa.

Haka kuma, ya ja kunnen jami’an ’yan sanda da su kiyaye sanya hannunsu a mummunar dabi’ar karɓar cin hanci ko zaluntar al’umma a gari.

Ya ce duk jami’in da aka kama zai ɗanɗana ƙudarsa domin hakan ya zama izina saboda idan ba tare da haɗin kan jama’a ba aikin su ba zai yi nasara ba.

Leave a Reply