Connect with us

Ƙasashen Waje

An gano wani babban kabari a Asibitin Al Shifa da ke Gaza — Rahoto

Published

on

An gano wani babban kabari a Asibitin Al Shifa da ke Gaza, a cewar wani rahoton Al Jazeera Arabic. Ma’aikatar Lafiya ta Gaza da Rundunar Ƴan-kato-da-gora ne suka gano kabarin.

Gidan talbijin ɗin da ke ƙasar Qatar ya ce an tono gawawwaki tara ranar Litinin a wajen asibitin da ke yammacin Gaza, sai dai jami’an kiwo lafiya sun dakatar da ci gaba da tono gawawwakin saboda fargabar da suke yi kan yiwuwar fuskantar hari daga jirage marasa matuƙa na Isra’ila da ke shawagi a yankin.

Gawawwakin da aka tono, waɗanda ba su gama ruɓewa ba, sun nuna cewa dakarun Isra’ila ba su jima da “kashe” mutanen ba, kuma alamu sun nuna cewa wasunsu marasa lafiya ne domin kuwa akwai bandeji a jikinsu, a cewar rahoton.

Dangin wasu daga cikin mutanen da aka tono gawawwakinsu sun gane ƴan’uwansu cikinsu har da wani dattijo da wata mace da kuma wani matashi ɗan kimanin shekara 20.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta sake kai harin bama-bamai a asibitocin Al Shifa da Al Nasr na Gaza

Ma’aikatan asibitin da likitoci sun bayyana cewa an kashe mutane da dama a wajen babbar ƙofar shiga asibitin, wadda ake kira ƙofa mai lamba 80. Kazalika ma’aikatan lafiya sun ce sun ga lokacin da dakarun Isra’ila suka kashe wasu mutanen.

A kwanakin baya ne dakarun Isra’ila suka janye daga Asibitin Al Shifa da ke Birnin Gaza bayan sun kwashe mako biyu suna mamaye shi, kuma sun ce sun yi ba-ta-kashi da mayaƙan Hamas a cikin asibitin da a baya ake kallo a matsayin babbar cibiyar kiwon lafiya ta Falasɗinawa.

Ganau sun ce sojojin Isra’ila sun kashe tare da jikkata mutane da dama kafin su janye daga asibitin. Haka kuma sun lalata ginin asibitin da gine-gine da ke maƙwabtaka da shi.

Kazalika sojojin Isra’ila sun lalata sashen da ake kula da masu fama da cutar ƙoda da sashen da ake karbar haihuwa da mutuware da wuraren da ake kula da masu cutar kansa da waɗanda suke fama da ƙuna, in ji shaidu.

A cewar wasu majiyoyin ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasɗinu, yanzu asibitin ba ya aiki kwata-kwata kuma sojojin Isra’ila sun lalata dukkan nau’urorin asibitin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Ƙasashen Waje

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Published

on

Harin ta'addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Harin ta’addanci ya kashe sama da mutane 20 a Mali

Wani hari da ake kyautata zaton masu ikirarin jihadi ne suka kai ƙauyen Djiguibombo da ke kusa da garin Bandiagara a yankin tsakiyar ƙasar Mali, ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula 20, kamar yadda wasu hukumomin yankin biyu suka tabbatar.

Majiyoyin da suka nemi a sakaya sunansu sun tabbatar da mutuwar mutane 20, sannan suka ce yadda lamuran tsaro suka taɓarɓare a yankin, ya hana jami’an tsaro kai ɗauki wajen.

Wani jagoran matasan yankin shi ma da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun a farkon daren ranar Litinin ɗin data gabata ne maharan suka kai farmakin, inda suka kwashe tsawon sa’oi uku a cikin garin.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe ‘yan jarida 106 a yakin da take yi a Gaza — Jami’ai

Ya ce sama da mutane 20 ne aka kashe a harin, kuma fiye da rabinsu matasa ne inda aka ranke musu harsuna.

Kasar Mali dai na fama da matsalolin tsaro na ƙungiyar Al-Qaeda da kuma na IS tun a shekarar 2012, inda ya bazu kasashen Burkina Faso da Nijar da ke makwabtaka da ita.

Tun bayan ƙwace mulki da sojoji suka yi a kasar a shekarar 2020, hukumomi  ke jin tsoron fitowa fili su sanar da labarin hare-haren ta’addancin da ake kai wa kasar da ke Yammacin Afrika.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Published

on

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama - Ministan Tsaron Isra'ila

A shirye muke mu yaƙi Hizbollah idan har ta kama – Ministan Tsaron Isra’ila

Ministan Tsaron Isra’ila Yoav Gallant ya ce sojojin Isra’ila za su kasance a shirye don daukar duk wani matakin da ya dace kan ƙungiyar Hizbullah ta ƙasar Labanon, ko da yake abin da ake so shi ne cimma matsaya ta shawarwari.

Muna kai wa ƙungiyar Hizbullah hari sosai a kowace rana kuma za mu kai ga cikakken shiri na ɗaukar duk wani mataki da ake buƙata a ƙasar Labanon, ko kuma cimma wani shiri daga matsayi mai ƙarfi.

KU KUMA KARANTA: Gaza ya zama gidan marayu kuma maƙabartar yara mafi girma a duniya – Emine Erdogan

Mun fi son tsari, amma idan aka kai mu maƙura za mu san yadda za mu yi yaƙi,” an ruwaito Gallant a wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.

Continue Reading

Ƙasashen Waje

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Published

on

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Mutum 12 ne suka mutu, 20 suka jikkata a wani hari da aka kai wata kasuwa a Yammacin Sudan

Aƙalla mutum 12 ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a jiya Laraba a wani hari da aka kai kan wata kasuwar dabbobi da ke El Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa a Yammacin Sudan.

A wata sanarwa da kwamitin sulhu na kwamitocin ‘yan gwagwarmaya na El Fasher ya fitar ya ce “harbin bindigogi a kasuwar dabbobi da ke birnin El Fasher ya yi sanadin mutuwar fararen hula 12 da kuma wasu 20 da suka samu raunuka daban-daban.”

Tun da fari a ranar Larabar da safe, kwamitocin ‘yan gwagwarmaya sun ce dakarun Rapid Support Forces (RSF) sun kai mummunan hari El Fasher da manyan bindigogi.

Tun a ranar 10 ga Mayu, aka fara ƙazamin fada tsakanin sojojin Sudan da RSF a El Fasher. Majalisar Dinkin Duniya da ƙungiyoyin agaji na ƙasa da ƙasa ke amfani da birnin a matsayin cibiyar ayyukan jinƙai ga yankin Darfur.

Rikicin Sudan ya ɓarke ne a cikin watan Afrilun 2023 tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo kan yarjejeniyar shigar da RSF cikin rundunar soja.

KU KUMA KARANTA: Adadin mutanen da suka rasa muhalli a sassan duniya ya zarta miliyan 114 — MƊD

Ya yi sanadin mutuwar mutum sama da 16,000, da raba kusan mutum miliyan 10 da muhallansu, sannan sama da miliyan 25 na buƙatar agajin jinƙai, lamarin da ya zama mafi girma a duniya ta ɓangaren matsalar rashin matsuguni da yunwa, a cewar MƊD.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like