An gano gawar ɗalibar aikin jarida Emanuel Kefas a gidan saurayinta a Taraba

0
209
An gano gawar ɗalibar aikin jarida Emanuel Kefas a gidan saurayinta a Taraba

An gano gawar ɗalibar aikin jarida Emanuel Kefas a gidan saurayinta a Taraba

Daga Jameel Lawan Yakasai

An gano gawar Emmanuel Kefas, saurayin marigayiya Comfort Jimtop, ɗalibar koyon aikin jarida a Jami’ar Taraba, a ƙauyen Tudiri da ke ƙaramar hukumar Ardo-Kola, lamarin da ya ƙara tayar da hankula a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Taraba, James Lashen, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Asabar.

Ya ce dagacin Tudiri ne ya sanar da ’yan sanda game da gano gawar a ranar Juma’a.

Lashen ya bayyana cewa an samu wayar Tecno a gefen mamacin, inda bayan bincike aka gano hotonsa tare da marigayiya Comfort Jimtop, inda aka ci gaba da bincike aka gano suna da alaƙar soyayya.

KU KUMA KARANTA: An tsinci gawar yaro da ruwa ya taho da shi a gadar Nahuta Potiskum

Ya ce, an kai gawar zuwa Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) Jalingo domin yin gwajin autopsy, yayin da ake ci gaba da tattara bayanai daga iyalan mamacin.

Rundunar ƴan sanda ta ce har yanzu ba a tabbatar da musabbabin mutuwar su ba, shin ko kashe-kai ne, kisa ko haɗari.

Tun da farko, mutuwar Comfort Jimtop ta haddasa zanga-zanga a Jami’ar Taraba da wasu sassan jihar, inda ɗalibai da kungiyoyin kare hakkin ɗan adam suka bukaci a gurfanar da wadanda ake zargi.

Kefas shi ne babban wanda aka riƙa zargi kafin gano gawarsa.

Leave a Reply