An gano baraguzan jirgin da ya faɗa ruwa a Fatakwal

0
63
An gano baraguzan jirgin da ya faɗa ruwa a Fatakwal

An gano baraguzan jirgin da ya faɗa ruwa a Fatakwal

Hukumar bincike da kiyaye haɗurra ta Najeriya (NSIB) ta ce an gano baraguzan jirgin sama mai sauƙar ungulu da ya faɗi a teku a Fatakwal da ke jihar Ribas.

A ranar 24 ga watan Oktoba, jirgin ɗauke da mutum takwas, fasjinja shida da matuƙa biyu ya faɗi a yankin ruwan Bonny Finima.

KU KUMA KARANTA:Wani jirgi da NNPCL ya ɗauka ya yi hatsari a Fatakwal

Tuni dai an gano gawarwakin mutum biyar da aka tsamo daga ruwa. Kamfanin man fetur na NNPCL a Najeriya ya ce shi ne ya dauki shatar jirgin.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, Darektar yada labarai da tallafawa iyali a hukumar ta NSIB Mrs. Bimbo Oladeji ta ce an gano jirgin ne a zurfin ruwan da ya kai mita 42 a cewar jaridun Najeriya

Rahotanni sun ce gwanayen ninƙaya ne suka gano baraguzan jirgin.

Leave a Reply