An farfasa katon ɗin giya 22, an kama mutane 79 a Yobe

1
342

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugabar ƙaramar hukumar Fika ta jihar Yobe, Hajiya Halima Kyari Joɗa, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, Hisbah da shugabannin gargajiya, sun lalata katan 22 na barasa, tare da kama wasu mutane 79 da ke da hannu a haramtaccen gidan raye-rayen da aka fi sani da “ Gidan Gala”.

An gudanar da samamen ne a ranar Litinin a garin Ngalda, ƙarƙashin jagorancin shugabar ƙaramar hukumar.

Kakakin shugaban ƙungiyar, Abubakar Ayuba Idris, wanda ya tabbatar da hakan, ya ce garin Ngalda ya shahara wajen kasuwanci da noman rani, kuma mazauna garin sun bayyana damuwarsu kan yadda lamarin ke lalata tarbiyyar ‘ya’yansu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun tabbatar da mutuwar abokai shida bayan sun sha giya a Ogun

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC) reshen jihar Yobe, Adamu Garba, ya ce rundunar haɗin guiwa ta NSCDC, JTF, DSS, NPF, Hisba, da ‘yan banga ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙaramar hukumar sun ƙwace kwalayen barasa da haramtaccen gidan Gala a garin Ngalda da ke ƙaramar hukumar Fika.

Ya ce a yayin samamen, an kama mutane 92 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban kamar sayar da barasa, sayar da wiwi, sayar da wuƙaƙe, baka da kibau da sauransu. Waɗanda aka kama ɗin, sun haɗa da maza 45 da mata 47.

1 COMMENT

Leave a Reply