An fara tattauna biyan diyyar harin Mauludi

0
110

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya ce sun fara tattaunawa da Gwamnatin Tarayya kan yadda za a biya diyya ga mutanen da harin jirgin soji a taron Mauludi ƙauyen Tudun Biri ya shafa.

Uba Sani, yi alƙawari a ranar Alhamis na tabbatar da ganin cewa an biya su diyya tare da tallafa wa waɗanda abin ya shafa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya ziyarci waɗanda harin bom ɗin ya shafa da suke kwance a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko inda yajajanta musu.

Shettima ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya sha alwashin hukunta duk masu hannun a harin bon ɗin da jirgin sojin ya kai, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 100.

Mataimakin shugaban ƙasan ya cen nan ba da dadewa ba,  Tinubu zai karɓi sakamakon binciken kwamitin da ya kafa domin gano musabbabin harin jirgin sojin a Tudun Biri.

KU KUMA KARANTA: Fastoci sun ziyarci waɗanda harin bom ɗin Mauludi ya shafa a Asibiti

Daga nan, ya miƙa wa gwamnatin jihar gudunmuwar miliyan 20 daga aljihun shugaban ƙasa, ga waɗanda harin Mauludin na Tudun Biri ya shafa, sannan shi ma ya ba da miliyan 10.

Shi ma Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajuddeen ya ba su tallafin miliyan 10 daga aljihunsa, ya kuma yi alƙawarin gina makaranta da asibiti a garin na Tudun Biri.

A jawabin mataimakin shugaban ƙasan, ya rantse da cewa Shugaba Tinubu yana da manufa kyakkyawa ga yankin Arewacin Najeriya na da ma ƙasar baƙi ɗaya.

Shettima ya ce “Wallahi [Tinubu] yana da kyakkyawar niya ga al’ummar Arewa duk da maganganu da wasu ke yi .

“A lokacin da wannan abin ya faru ya ƙira ni kusan sau 17 saboda a lokacin yana Dubai wurin taro domin yana son ya ga an kawo tallafi ga mutanen da abin ya shafa.”

Ya bayyana cewa Gwamnatin Tinubu za ta gina gidaje guda 1,000 a Jihar Kaduna, a ƙarƙashin shirinta na Fulako da nufin magance matsalar tsaro.

Ya ce gidaje 500 a za a gina su ne Kudancin jihar, sauran 500 kuma a Arewacin jihar a karkashin shirin na Yaki da Ta’adanci, wanda kuma kowa da kowa ne za su amfana da gidajen.

Shettima ya bayyana cewa shirin Fulako da Gwamnatin Tarayya ta ɓullo da shi zai taimaka wajen magance matsalar tsaro a Arewa Maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

Ya lisssafo jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara da Katsina da Kaduna da Binuwe da Neja a matsayin waɗanda da za su amfana.

Leave a Reply