Rahotanni sun ce tuni aka fara rufe manhajojin hada-hadar kuɗaɗe na intanet, ko kuma cryptocurrency a Turance, bisa umarnin hukumomin ƙasar, a wani mataki na daƙile hauwhawar farashin dala da faɗuwar darajar naira.
A ranar Laraba ne hukumomi suka bai wa kamfanonin waya na ƙasar umarnin toshe damar shiga manhajojin, domin hana masu hada-hadar kuɗaɗe ta intanet damar shiga su yi cinikayya.
Masu musayar kuɗaɗe a ƙasar da kuma hukumomi na zargin masu hada-hadar kudi ta intanet da ba da gagarumar gudunmuwa wajen tashin farashin dala a kasar, abin da ya jefa tattalin arzikin kasar cikin wani mawuyacin hali.
Wata majiya daga Hukumar Kula da Sadarwa ta Najeriya NCC ta tabbatarwa TRT Hausa cewa an bai wa kamfanoni na waya umarnin daukar matakin, kuma har ma an fara aiki da shi, musamman ga masu amfani da waya.
Wasu jaridun Najeriya sun rawaito cewa kamfanonin sadarwa na kasar sun tabbatar da samun umarnin daga NCC don su dauki matakin.
Manyan kamfanin da matakin ya shafa a cewar bayanan sun hada da Binance, da Forextime, da OctaFX, da Crypto, da FXTM, da Coinbase, da kuma Kraken.
KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Legas za ta fara ciyar da mutane dafaffen abinci kyauta
To sai dai su ma a na su ɓangaren, tuni kamfanoni na hada-hadar kuɗaɗen ta intanet suka fara ɗaukar matakan daƙile cinikayya tsakanin dala da naira barkatai.
Wannan matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka shi ne na baya-bayan nan a cikin jerin matakan da take ɗauka don magance tashin farashin dala, abin da yake haifar da tashin gwauron zabi na kayan masarufi a kasar.
Batun dai na ci gaba da janyo damuwa a tsakanin yan ƙasar baki ɗaya, musamman masu ƙaramin ƙarfi, waɗanda a mafi yawan lokuta abincin da za su ci a cikinsu ke gagararsu.