No menu items!

Sample Page Title

Date:

An dakatar da wasu jami’an gwamnatin Kaduna, bisa bayar da bayanan ƙarya

Kotun ɗa’ar ma’aikata ta bayar da umarnin dakatar da wasu manyan jami’an jihar Kaduna guda uku biyo bayan zargen da ake musu na ba da bayanan ƙarya wurin bayyana kadarorinsu, yayin da suke jira su gurfana gaban kotu.

A wata sanarwa da hukumar ɗa’ar ma’aikata (CCB) ta fitar a ranar Alhamis, ta umarci Samuel Peter, kwamishinan tsaro na cikin gida mai riƙo da Shizzer Bada, kwamishinan kuɗi da kuma Tijjani Abdullahi, shugaban hukumar kula da ilimin bai ɗaya ta jiha, da su sauƙa daga muƙamansu.

Umarnin da aka fitar a ranar 22 ga watan Oktoba, ya biyo bayan ƙarar ɓangare ɗaya ne da hukumar CCB ta shigar a kotun.

Ana sauraren irin wannan ƙara a kotu ba tare da ɓangaren da ake zargi yana nan a kotu ba.

KU KUMA KARANTA:Gwamna Uba Sani ya ziyarci ɗaliban makarantar Kuriga da aka sako (Hotuna)

Ana zargin jami’an ne da karya dokar CCB da CCT wadda ta buƙaci jami’an gwamnati su bayyana hakikanin kadarorinsu a hukumance daga lokaci zuwa lokaci.

Hukuncin kotun zai ci gaba da aiki har zuwa lokacin da za a saurari karar da hukumar ta shigar a ranar 21 ga watan Oktoba, tare da tuhume-tuhume kan jami’an.

Sanarwar ta ce kotun ta kuma umurci gwamnan jihar Kaduna da sakataren gwamnatin jihar da su nada ma’aikata na wucin gadi da za su maye gurbin jami’an da aka dakatar da su.

“Kotu ta zartar da wannan hukuncin ne a ranar 22 ga Oktoba, 2024, biyo bayan wata takardar da Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata, wato ‘Code of Conduct Bureau’ a turance, ta gabatar dangane da zargin rashin mutunta dokar da’ar ma’aikata ta, CAP C1 LFN 2004,” in ji Veronica Kato, kakakin hukumar a wata sanarwar.

An shirya jami’an uku za su bayyana a gaban kotun ranar 7 ga watan Nuwamba.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...