An dakatar da shugaban ‘Civilian JTF’ a Borno kan zargin awun gaba da motocin Hilux

Rundunar Civilian Joint Task Force a jihar Borno ta dakatar da shugabanta, Lawan Ja’afar, bisa zargin karkatar da motocin da gwamnatin jihar ta bai wa ƙungiyar.

Babban mai bincike na ƙungiyar Bashir Abbas ne ya sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Maiduguri ranar Lahadi.

Malam Abbas ya ce an cimma wannan matsayar ne bayan gudanar da taruka da tattaunawa da shugabanni da mambobin ƙungiyar suka yi.

Da ya ke bayar da misali da doka ta 6 (vi) na kundin tsarin mulkin CJTF, ya ce shugabanni baki ɗaya sun yanke shawarar dakatar da Mista Ja’afar, wanda ake zargi da karkatar da wasu motocin Hilux da gwamnatin Borno ta bai wa ƙungiyar domin gudanar da ayyuka.

KU KUMA KARANTA: Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Gwale

“Ya kuma karkatar da wasu motoci ƙirar Hilux guda biyu da NNPCPL ta bai wa ƙungiyar don gudanar da ayyukan su ma.

“Shugabannin na kuma sanar da jama’a matakin da ta ɗauka bisa ga doka ta 6, doka ta 1 na kundin tsarin mulkin CJTF, na naɗa Baba Shehu Abdulganiyu a matsayin shugaban riƙo na ƙungiyar, wanda ya ninka a matsayin Kwamanda Sashe 4 na CJTF.

“Baba Shehu ne zai zama shugaban ƙungiyar har sai an naɗa shugaba mai inganci.

“Shugabannin sun kuma yanke shawarar mayar da Babakura Mustapha, Abba Aji Kalli, Abba Tijjani Sadiq da Barista Jibrin Tela Gunda wanda aka dakatar daga 2022, “in ji shi.

Da yake mayar da martani, Mista Jafar ya ce dakatarwar da aka yi masa ba za ta iya tsayawa ba saboda biyar ba ta cika adadin 27 ba.

Ya yi watsi da zargin cewa ya karkatar da motoci ƙirar Toyota Hilux guda 13 da gwamnatin Borno ta bayar, inda ya ce an sayar da motocin ga dukkan ‘yan ƙungiyar a matsayin tarkace, inda ya siyo wasu daga cikinsu.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *