Connect with us

Labarai

An dakatar da Sarkin Sasa kan rashin biyayya

Published

on

Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Zungeru ya sanar dakatar da Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin bisa zargin rashin biyayya.

Alfijir Labarai ta rawaito Olubadan, Oba Olalekan Balogun, ya dakatar da Sarkin Sasa, Alhaji Haruna Maiyasin kan zargin rashin biyayya.

Olu na Ibadan ya dakatar da Sarkin Sasa ne ta hannun Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Zungeru, bisa zargin bayar da sarautu ba tare da tuntuɓar Sarkin Hausawan ba.

An sanar da dakatarwar da aka yi wa Sarkin Sasa, wanda Hakimi ne a Masarautar Al’ummar Hausawa a Jihar Oyo ne a wani zama da Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Zungeru ya jagoranta a Sabo Ibadan.

KU KUMA KARANTA: Jam’iyar APC a Jigawa ta dakatar da wani shugaban jam’iyar a jihar, bisa zargin fyaɗe

Sarkin Hausawan ya yi zargin cewa zaman Hakimin na iya haifar da rikici a yankin, don haka aka dakatar da shi har zuwa lokacin da Majalisar Al’ummar Arewa da ke Ibadan ta yanke hukunci kan lamarinsa.

“A zamanin wana, Shuaibu Dikko III, a 1983 aka naɗa Alhaji Haruna Maiyasin a hakimi, wato Baale a ƙasar Yarbawa domin samun zaman lafiya da adalci a tsakanin al’ummar Hausawa da ke Sasa.

“Saboda haka, kuma don guje wa kowane irin rikicin ƙabilanci irin na Sabo-Sagamu, Sabo-Ile-Ife da kuma na Sasa da ke Ƙaramar Hukumar Akinyele, ni Alhaji Ali Zungeru, Sarkin Hausawa Ibadan da Majalisar Masarautar Arewa muka dakatar da Maiyasin daga hakimcin Hausawan Sasa,.

“Dalili shi ne saboda rashin ladabinsa, raina kujerar Sarkin Ibadan, da kuma ba da sarautun da yake yi ba tare da sahalewar Sarkin Hausawan Ibadan ba.

“Dakatarwar za ta ci gaba har zuwa lokacin da Majalsiar Al’ummar Arewa da ke Ibadan ta kammala nazarin lamarin,” in ji Sarkin Hausawan.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Al'ajabi

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Published

on

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon gini mai hawa 2 ya rushe a Legas

Wani sabon bene mai hawa biyu a Jihar Legas, ya rushe yayin da ake tsaka da mamakon ruwan sama wanda ya haddasa ambaliya a wasu sassan jihar.

Ginin ya rushe ne a lamba 12 da ke yankin Cameroun kusa da Ewenla a Mushin.

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (LASEMA), ta bayyana cewar bayan isar jami’anta wajen da lamarin ya faru, ta gano wani sabon gini mai hawa biyu ya rushe.

An ceto mutum bakwai; mata uku da maza huɗu, tuni aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

KU KUMA KARANTA: Wani bene mai hawa 4 ya rufta da mutane a Abuja

Ya zuwa yanzu dai hukumar, ta ce babu wanda ya mutu a dalilin rushewar ginin.

Babban sakataren LASEMA, Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce ana ci gaba da gudanar aikin ceto don tabbatar da babu wanda ya maƙale a baraguzai.

Continue Reading

Labarai

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Published

on

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Wani jami’in EFCC ya hallaka kansa a Abuja

Rahotanni sun bayyana cewar wani jami’in Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa (EFCC), ya hallaka kansa har lahira a Abuja.

An tsinci gawar marigayin ne a gidansa da ke babban birnin tarayya.

Marigayin, wanda ba a bayyana sunansa ba, an ce ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi kwas na 5 a makarantar horas da masu yi wa ƙasa hidima ta hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa.

An ruwaito cewar yana da ƙwazo da himma a wajen gudanar da ayyukansa.

Wata majiya ta ce jami’in ya jima yana fama da baƙin ciki da matsalolin rayuwa kafin mutuwarsa.

Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar za ta binciki musababbin da ya sanya ya kashe kansa, kuma hukumar za ta taimaka wa iyalansa.

Oyewale, ya ƙara da cewa hukumar za ta binciki wasu abubuwa da suka haɗa da matsalar taɓin hankali da kuma matsalolin iyali waɗanda ka iya sanya ma’aikacin kashe kansa.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin wani jami’in kwastam ya kashe kansa a Abuja

Sai dai ya ce hukumar ba za ta fitar da wata sanarwa ko kuma bayyana sunan jami’in ba, har sai an kammala bincike.

Continue Reading

Labarai

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Published

on

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC), ta rufe shaguna kusan 100 a babbar kasuwar Ogbete ta Jihar Enugu, bisa zargin sayar da wasu abubuwan sha na jabu.

Daraktan NAFDAC, Martins Iluyomade a yankin Kudu maso Gabas, ya ce hukumar ta ɗauki matakin ne bayan wani samame da ta kai a ranar Litinin.

A yayin samamen jami’an hukumar NAFDAC, sun cafke wata babbar mota ɗauke da kayayyakin maye tare da cafke wasu ‘yan kasuwa huɗu da ake zargi da hannu wajen sayar da jabun abubuwan sha.

Iluyomade, wanda masanin haɗa magunguna ne, ya nanata cewa matakin ya zama dole domin kare masu amfani da ire-iren kayayyakin .

Ya ce waɗanda ake zargin a halin yanzu ana kan bincikensu kuma za su fuskanci tuhuma a gaban kotu bayan kammala binciken.

KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J

Har wa yau, ya nanata ƙudurin NAFDAC na kawar da kayayyaki marasa inganci, da jabun abubuwan ci da sha, da gurɓatattun kayayyaki a kasuwa.

Ya ƙara da cewa, an gudanar da binciken ne tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro.

A gefe guda kuma, ya bayyana muhimmancin aikin hukumar na tabbatar da lafiyar al’umma.

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like