An dakatar da sabuwar dokar haraji a Najeriya
Daga Ibraheem El-Tafseer
Majalisar Dattawa ta dakatar da ci gaba da yunƙurin zartar da ƙudurin sabuwar dokar haraji har sai kwamitin kuɗi na majalisar ya zauna da ofishin ministan shari’a don yin gyararraki a wasu sassa na sabuwar dokar.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ne ya ba da umarnin a zaman majalisa na yau Laraba.
KU KUMA KARANTA: Dokar Haraji: Tinubu ya umarci Ma’aikatar Shari’a da Majalisar Dokoki su yi aiki tare