No menu items!

Sample Page Title

Date:

An ci tarar TikTok dala miliyan 10 a kan gasar yin bidiyon da ya jawo mutuwar yara

Kotun Ƙolin Venezuela ta ci tarar kamfanin TikTok dala miliyan 10 saboda “rashin aiwatar da matakan” kare yaɗuwar wani bidiyo na gasa da aka saka wanda ake zargin yaɗuwwarsa ta yi sanadiyar mutuwar yara uku ‘yan Venezuela kwanan nan.

Mai Shari’a Tania D’Amelio ta fada a ranar Litinin cewa TikTok ya yi sakaci kuma ta bai wa kamfanin kwana takwas kacal don ya biya tarar.

Kotun Ƙolin Venezuela ta ci tarar kamfanin TikTok dala miliyan 10 saboda “rashin aiwatar da matakan” kare yaduwar wani bidiyo na gasa da aka saka wanda ake zargin yaduwwarsa ta yi sanadiyar mutuwar yara uku ‘yan Venezuela kwanan nan.

Mai Shari’a Tania D’Amelio ta fada a ranar Litinin cewa TikTok ya yi sakaci kuma ta bai wa kamfanin kwana takwas kacal don ya biya tarar, yayin da ta kuma umarce shi da ya bude ofis a Venezuela wanda zai kula da masu amfani da shi don tabbatar da bin dokokin kasar.

Alkaliyar ba ta bayyana ta yadda Venezuela za ta tilasta wa TikTok, wanda babban ofishinsa ke China ba tsarin biyan tarar.

KU KUMA KARANTA: Hukumar FCCPC ta ci tarar kamfanin Meta dala miliyan 220 a Najeriya

Venezuela ta toshe shafukan intanet da dama a shekarun baya saboda rashin bin ka’idojin da hukumar sadarwarta ta gindaya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Associated Press ya tuntubi TikTok amma har zuwa yanzu kamfanin bai amsa ba.

A watan Nuwamba ne shugaban ƙasar Venezuela Nicolas Maduro ya zargi TikTok da alhakin mutuwar wata yarinya ‘yar shekara 12 da ake zargin ta mutu bayan ta shiga wata gasar bidiyo a TikTok da ya shafi shan kwayoyin kwantar da hankali da hana rashin barci.

Ministan Ilimi na Venezuela Hector Rodriguez shi ma ya fada a watan da ya gabata cewa wani matashi dan shekara 14 ya mutu bayan ya shiga wata gasar da aka yi a TikTok wanda ya hada da shan abubuwa.

Kuma a ranar 21 ga Nuwamba, babban lauyan Venezuela ya ɗora alhakin mutuwar wani yaron a kan TikTok bayan shiga gasar.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...