An cafke ‘yan fashin babur da ke busa barkono a fuskar ‘yan okada kafin su karɓe babur

0
182

‘Yan sanda a jihar Legas sun cafke wasu ‘yan fashi da makami guda biyu da suka ƙware wajen fesa barkono domin yin fashi wa masu tuƙa babura.

Waɗanda ake zargin dai sun kai hari kan wani direban babur ne a ƙoƙarinsu na ƙwace masa babur din a lokacin da mazauna unguwar gadar Obasanjo da ke Alagbado suka kama su, suka miƙa su ga ‘yan sanda.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Ben Hundeyin, wanda ya tabbatar da kamun ya ce ‘yan sandan na bin sauran ‘yan ƙungiyar.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da kashe ɗan-fashin dajin da ya addabi jihohin arewa

“A ranar 15/02/24 da misalin ƙarfe 07:30 na safe, an samu rahoton wani direban babur cewa da misalin karfe 06:30 na safe wasu mutane biyu waɗanda aka bayyana sunayensu da Ayuba Oyegbele da Ojo Gbolahan suka tare shi a Ogo Oluwa, Alagbado.  ya kai su gadar Obasanjo,” in ji PPRO.

“Amma da isa ga gadar Obasanjo, Ojo Gbolahan ya sauƙo ya yi kamar yana son ya biya mai babur ne

“Amma a maimakon haka sai ya fito da busasshiyar barkono ya hura a idon mai babur kuma ana cikin haka ne sai biyun suka fara dukan mai babur da nufin su yi masa fashin babur.

“An yi sa’a, masu wucewa da suka ga yadda mai babur ke ihun neman agaji, sun zagaya don ceto shi, yayin da waɗanda ake zargin suka yi yunƙurin tserewa.

“An fi karfinsu aka cafke su aka kai su ofishin ‘yan sanda na Alagbado.

“Bincike ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun saba yi wa masu babura fashi,” ya ƙara da cewa.

Leave a Reply