An cafke waɗanda suka kitsa kashe-kashen Filato

0
194

’Yan sanda a sun cafke mutanen da ake zargi sun kitsa hare-hare da kashe-kashen kwanan nan a ƙananan hukumomin Mangu, Bokkos da Barikin Ladi na Jihar Filato.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato ta ce mutum 17 ne suka shiga hannun jami’anta kan harin ranar jaribirin Kirsmetin a kananan hukumomin uku inda aka kashe mutane kimanin 100.

Da yake gabatar da su ga manema labarai, Mataimakin Sufeto-Janar mai kula da Shiya ta 4, Ebony Eyibio, ya ce tara daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne kan zargin hannunsu a kashe-kashen Mangu, ragowar takwas ɗin kuma kan zargin kashe-kashe a Bokkos da Barikin Ladi.

Eyibio wanda kakakin rundunar, DSP Alabo Alfred, ya wakilta ya ce, “Ranar Alhamis da misalin ƙarfe 10 na dare aka tsegunta mana game da wasu da ke shirin kai hari a yankin Ntam da kuma ASTC da ke ƙarama hukumar Mangu.

KU KUMA KARANTA: Gwamnatin Filato ta sanya dokar hana fita na tsawon awa 24 a Mangu

“Shi ne zaratan jami’anmu suka kai samame suka daƙile yunƙurin kai harin.

“Hakazalika jami’anmu sun daƙile yunƙurin masu kona gidaje da wuraren ibada a yankin Panyam da taimakon wasu dattawan yankin.“

Leave a Reply