An cafke masu aikata laifuka daban-daban sama da 500 a Kano

0
54
An cafke masu aikata laifuka daban-daban sama da 500 a Kano

An cafke masu aikata laifuka daban-daban sama da 500 a Kano

Daga Shafa’atu Dauda Kano

A wani samame na haɗin gwiwa da hukumomin tsaro suka gudanar a faɗin jihar Kano, an cafke fiye da mutum 500 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da dabanci, fashi da makami, da fataucin miyagun kwayoyi. Haka kuma, an samu nasarar kwace miyagun kwayoyi da darajarsu ta kai Naira miliyan 300.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana cewa sama da mutum 150 daga cikin wadanda aka kama, suna da hannu cikin manyan laifuka da suka hada da kwacen waya da barna a cikin gari. Ya ce wannan aikin na musamman ya gudana ne a kananan hukumomi takwas na birnin Kano, bisa bayanan sirri da aka samu daga jami’an tsaro da al’umma.

KU KUMA KARANTA:A tabbata an bi haƙƙin waɗanda aka kashe a Edo, an kuma biya su diyya – Gwamnan Kano

Aikin, wanda aka yi tare da hadin gwiwar hukumar NDLEA, NSCDC, hukumar kula da gidajen yari, hukumar shige da fice, da sauran hukumomi, ya zama wani muhimmin mataki na yaki da ta’addanci da kuma matsalolin da ke addabar matasa.

Leave a Reply