No menu items!

Sample Page Title

Date:

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wani kwamishinan ‘yan sanda na bogi.

Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da kamun a ranar Litinin, 11 ga watan Satumba, yayin da yake yiwa manema labarai ƙarin haske kan nasarorin da rundunar ta samu a baya-bayan nan.

Ya ce an kama wanda ake zargin “CP na jabu”, mai suna Emmanuel, a ranar 2 ga Satumba, da misalin ƙarfe 4:40 na yamma a lokacin da ya ziyarci rundunar ‘yan sanda a yankin Ikorodu kuma ya gabatar da kansa a matsayin kwamishinan ‘yan sanda.

KU KUMA KARANTA: Ayi hattara da ‘hukumar EFCC na bogi’ – EFCC

“An martaba shi,  amma da aka tambaye shi, an gano shi kwamishinan jabu ne. A yayin bincike a gidansa, mun gano katin shaidar mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Kenwood walkie-talkie, camouflage na ‘yan sanda, singlet da hular fuska na yan sanda,” inji shi.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...