An cafke jami’in gidan yari kan zargin luwaɗi da ƙaramin yaro a Gwambe

0
286

’Yan sanda a jihar Gwambe sun kama wani hafsan hukumar gidajen yari da ke aiki a garin Bajoga na ƙaramar hukumar Funakaye kan zarginsa da yin luwaɗi da wani ƙaramin yaro.

Da yake gabatar da wanda ake zargin da wasu mutum 14 da ake zargi da laifuffuka daban-daban, kakakin rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce ’yan sandan sun kama wanda ake zargi da aikata luwaɗin ne bisa rahoton da aka kai musu.

Amma da wakilin mu yake zantawa da wanda ake zargin, ya bayyana cewa sharri kawai ake masa.

Jami’in gidan gyaran halin ya ce wani mutum ne da kawai bai yarda da mu’amallarsa da mutane ba a garin na Bajoga, ya masa ƙagen cewa ya yi luwaɗi da ɗansa.

KU KUMA KARANTA: Hisbah ta kama mata 15 da suka halarci bikin ‘yan luwaɗi a Kano

Ya ce an je asibiti likita ya gwada yaron da ake zarginsa da shi, amma gwajin bai nuna cewa an yi luwaɗi da shi ba.

Jami’in ya jaddada cewa ɓata masa suna aka yi , kuma Allah zai bi masa haƙƙinsa.

Ya ƙara da cewa duk da bai aikata hakan ba kuma yasan luwaɗi babban laifi ne, yana ƙira ga masu irin wannan hali da su daina.

Daga nan sai kakakin rundunar ’yan sandan ASP Mahid Mu’azu Abubakar ya ce da zarar sun kammala bincike za su tura wanda ake zargin zuwa kotu.

Leave a Reply