An buƙaci Najeriya ta dakatar da yarjejeniyar Shell

0
583

Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty International da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama a ranar Litinin sun yi ƙira ga gwamnatin Najeriya da ta dakatar da yarjejeniyar da kamfanin Shell ya yi na sayar da wasu kadarorinsa a matsayin wata hanya ta tabbatar da haƙƙoƙin al’ummar yankin.

Al’ummomin da ke noma da kamun kifi a yankin Neja-Delta, cibiyar samar da ɗanyen mai a Najeriya, sun shafe shekaru suna shari’a kan ɓarnar da malalar mai yake yi a yankin.

Kamfanin Shell ya amince ya sayar da kadarorinsa da ke gaɓar tekun ƙasar ga wata ƙungiya mai cibiya a Najeriya kan kuɗi dala biliyan 2.4 yayin da ya koma harkokin kasuwanci a ƙarƙashin teku.

KU KUMA KARANTA:Hamas da Islamic Jihad sun bayar da sharuɗa 4 na nasarar yarjejeniyar tsagaita wuta

A wata wasiƙa da aka fitar a ranar Litinin, Amnesty da sauran ƙungiyoyin kare haƙƙin Najeriya da na ƙasa da ƙasa sun yi ƙira ga hukumar da ke kula da harkokin Najeriya da ta ƙi amincewa da sayar da kadarorin Shell ga Renaissance African Energy.

Wasiƙar ta ce “Bai kamata a bar Shell ya yi waswasi da shari’a ba don guje wa alhakin da ya rataya a wuyansa na tsaftace gurɓacewa da ya bari,” in ji wasiƙar.

Ya ƙara da cewa, bai kamata a ba da izinin sayar da kadarorin Shell ba, sai dai idan har an tuntuɓi al’ummomin yankin, don a tantance gurɓacewar muhalli da aka yi a halin yanzu, da kuma samar da kuɗaɗen da za a kashe wajen tsaftace muhalli.

Shell bai amsa buƙatar yin sharhi nan take ba.

Kamfanonin mai sun ce suna gudanar da ayyukansu ne bisa tsarin mafi kyawun muhalli na fannin kuma suna zargin yawancin malalar da ake samu a kan zagon ƙasa da ɓarayin mai da ke fasa bututun mai.

Leave a Reply