Daga Haruna Abdulrashid
A ranar Laraba 20 ga Satumba, 2023 aka buɗe sabon Asibiti a kusa da gidan Marayu da ke Tunfure na jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin Hukumar Tallafawa Jama’a ta CSDA, kuma tare da goyon baya na Mata masu tagaza wa Da’awa, inda aka samu manyan baƙi har Matan ‘yan siyasa da ‘yan Kasuwa da sauran muƙarraban Gwamnati.
Haka zalika an karrama wasu bayin Allah waɗanda suke bayar da taimako a kowane lokaci wa gidan Marayun.
A jawabin shugaban ƙungiyar Da’awa, Malam Lawan Muhammad ya bayyana nasarori da ƙalubalen da suke samu a ɗawainiyar gidan Marayun.
Yayin da Shaikh Albany Gombe ya gabatar da Lacca mai taken, “Gudumawar al’umma a harkar kiwon lafiya”
Haka shi ma mai Martaba Lamiɗo Gona (Sarkin Gona) ya yi ƙira musamman ga al’umma da su guji cinye dukiyar Marayu, kuma ya yi alƙawarin bayar da gudumawarsa a kowane lokaci.
Dakta Habu Ɗahiru (tsohon Kwamishina na Lafiya) ya yi alƙawarin saka dukkan kayan shimfiɗa a cikin Asibitin.
KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun buɗe sakatariyar karamar hukumar Filato
Sannan Farfesa Sadeeq shi ma ya yi alƙawarin saka dukkan kayan zama na cikin Asibitin.
An gabatar da kyaututtkan yabo ga waɗanda suka daɗe suna taimakawa Marayun.
Hajiya Habiba Ibrahim Joɗi, Uwargidan Sakataren Gwamnati ita ta buɗe Asibitin a madadin Uwargidan Gwamnan Jiha Hajiya Asama’u Inuwa.
Daga ƙarshe shugabannin Da’awa sun yi godiya ga dukkan al’umma da suka bayar da gudumawa na dukiya da shawarori da addu’a har ma da waɗanda suka amfana da wannan lamari.