An bayyana kuɗin da maniyyata aikin hajjin 2024 za su ajiye a Kano

0
268

Hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano ta ƙaddamar da shirye-shiryen aikin hajjin shekarar 2024 a hukumance.

Alfijir Labarai ta rawaito Darakta Janar na hukumar Alhaji Laminu Rabi’u ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai, wanda ke alamta fara shirye-shiryen aikin na bana a gudanar a ofishinsa .

Laminu ya ce hukumar alhazai ta ƙasa NAHCON ta ware kujeru 5,934 ga jihar Kano.

Bisa umarnin hukumar NAHCON, kashi 60 cikin 100 na kujerun aikin Hajjin bana za a baiwa alhazai ne yayin da za a baiwa maniyyatan da ke adashin gata a ƙarƙashin bankin musulunci na Ja’iz kashi 40 cikin 100.

Har ila yau, Darakta Janar ɗin ya sanar da Naira miliyan 4 da rabi a matsayin kuɗin da maniyyata za su fara ajiyewa na aikin Hajjin baɗi, inda ya ƙara da cewa waɗanda ba za su iya ba to su hanzarta shiga shirin adashen gata.

KU KUMA KARANTA: Maniyyatan jihar Kaduna za su biya kuɗin kujerar hajji cikin wata biyu

Ya ce “mun ƙaddamar da shirin tsare-tsaren aikin Hajjin 2024 a yau. Mun ƙaddamar da sayar da kujerun ne bayan mun kammala rabon kashi 60 na kujerun zuwa ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano.

“Mun umurci jami’an alhazai na ƙananan hukumomi da su fara karɓar kuɗaɗen ajiya daga maniyyatan da ke da niyyar zuwa ƙasar mai tsari domin saukƙe farali,” inji shi.

Rabi’u Dan Bappa ya kuma ce hukumar ta tashi tsaye wajen ganin an mangace dukkan ƙalubalen da aka fuskanta a aikin Hajjin 2023 domin gudanar da aikin na bana cikin nasara.

Darakta janar ɗin ya ba da tabbacin za su baiwa maniyatan da ba su sami zuwa a aikin hajjin 2023, fifito sai dai idan su suka ce ba sa buƙata, suna buƙatar kuɗaɗensu.

Leave a Reply