An bayyana inda za a saurari shari’ar zaɓen gwamnan Kano da na sauran jihohi

0
277

Shugabar kotun ɗaukaka ƙara, Mai Shari’a Monica Dongban-Mensem, ta miƙa dukkan ƙararrakin zaɓe da ke gaban kotun a jihohi 36 zuwa rassan kotun ɗaukaka ƙara dake Abuja da Legas.

Rahotanni na cewa duk wasu ƙararrakin da aka ɗaukaka na daga hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe daban-daban na jihohi 36 na ƙasar za a saurare su kuma za a tantance su a rassan kotun da ke Abuja da Legas.

Bisa ga wannan mataki na Dongban-Mensem, cikin rassan kotun ɗaukaka ƙara guda 20 da ake da su a ƙasar, guda biyu kaɗai cikin kotun za su saurari duk wasu ƙararrakin da suka taso bayan hukuncin kotun sauraron ƙararrakin zaɓe a duk faɗin ƙasar.

Umurnin ya shafi zaɓukan gwamnoni, na ‘yan majalisun tarayya da na jihohi.

KU KUMA KARANTA: INEC ta musanta janyewa daga ɗaukaka ƙarar Abba kan Gawuna

Mensem ta yi hakan ne a matsayin mayar da martani ga ɗimbin koke-koke da zanga-zangar da wasu jam’iyyun siyasa da ‘yan takararsu suka yi, inda suka yi zargin cewa gwamnonin jihohi sun kawo cikas ga alƙalan kotunan yayin shari’ar a tarabunal.

Rahotanni sun nuna cewa mai shari’a ta ƙaddamar da bincike mai zurfi kan zargin da ake wa gwamnoni da alƙalan kotun sauraron ƙararrakin zaɓe.

Binciken da aka yi ya tabbatar da gaskiyar zarge-zargen ƙulla alaƙa tsakanin wasu gwamnoni da alƙalan kotuna, wanda ya kai ga gurɓata hukuncin Shari’un da kotun suka yanke.

Rahotanni sun bayyana cewa an gurfanar da wasu alƙalan kotunan kotun, kuma suna iya fuskantar tuhuma daga hukumar kula da harkokin shari’a ta ƙasa (NJC).

Leave a Reply