An bai wa ‘yan Kenya hutu domin su shuka bishiya miliyan 100

0
171

An bai wa ƴan Kenya hutu na musamman domin shuka bishiya miliyan 100 a wani ɓangare na zimmar gwamnatin ƙasar na ganin an shuka bishiya biliyan 15 a cikin shekara goma.

Hutun zai bai wa ‘dukkan wani ɗan Kenya damar shuka bishiya”, a cewar ministar muhalli Soipan Tuya.

Shugaba William Ruto ya jagoranci shirin shuka bishiyan a garin Makueni da ke gabashin ƙasar.

Ya buƙaci kowane ɗan Kenya ya shuka aƙalla bishiya biyu, domin kai wa miliyan 100 da ake hankoro.

KU KUMA KARANTA: Saboda matsalar tsaro, mutanen Jibiya sun fara sare bishiyoyin kan hanya

Gwamnatin ƙasar ta ce hakan zai taimaka wajen yaƙi da sauyin yanayi.

Ta ce itatuwa na taimakawa wajen daƙile ɗumamar yanayi ta hanyar fitar da gurɓataccen hayaki na carbon.

Gwamnatin ta ce za ta samar da bishiyoyi miliyan 150 a makarantu.

An aike da ministoci zuwa sauran larduna domin jagorantar shirin tare da gwamnonin larduna da kuma was jami’an gwamnati.

Sai dai, da wuya mutane da yawa, musamman ma a birane su shiga shirin na shuka bishiya, inda za su yi amfani da hutun domin yin wasu ayyukansu.

Leave a Reply