Babban bankin Najeriya (CBN) ya cire takunkumin da ya ƙaƙaba wajen shigo da wasu kayayyaki tun shekarar 2015.
Sanarwar da babban bankin ya fitar ta bakin Dskta Isa Abdulmumin a shafukansa a ranar Alhamis ya yi bayanin matakin da aka dauka.
Rahoton ya tattaro jerin duka sunayen kayayyaki da yanzu ya halasta ɗan kasuwa ya samu kuɗi domin ya shigo da su.
Kafin yanzu, jaridar ‘The Cable’ ta ce masu buƙatar sayo waɗannan kaya daga ƙasashen ƙetare, suna neman kuɗi ne da tsada a kasuwar canji.
CBN ya yi hakan ne domin yunƙurin tallafawa kamfanonin gida da su ke samar da waɗannan kaya da kuma tsare mutuncin Naira.
KU KUMA KARANTA: Ƙasar Gabon ta sake buɗe iyakokin ƙasar – Sojoji
Ga jerin kayan nan kamar haka:
Kayan da CBN ta cirewa takunkumi
- Shinkafa
- Siminti
- Bota
- Kayan man gyaɗa, man ja da sauransu
- Nama da kayan nama
- Ganye da sauran kayan ganye
- Kaji, ƙwai, zabi
- Jiragen sama/jiragen yawo
- Turaren wutan Indiya
- Kifin gwangwani
- Naɗaɗɗen rodi
- Shafaffen rodi
- Kwanon gini
- Baro
- Kwanon ɗaukar kaya
- Akwatin ƙarfe da garwa
- Kayan tangaran
- Gangunan ƙarfe
- Bututun rodi
- Wayoyin rodi
- Rodi
- Ƙarfen waya
- Ƙusoshi
- Wayar tsaro
- Allon katako
- Faifen allo
- Filai wood
- Ƙofofin katako
- Kayan jeren gida
- Tsinken sakace
- Gilas
- Kayan girki
- Kayan tebura
- Tayil
- Tufafi
- Kayan auduga
- Yadi/shaddoji/leshi da saurasu
- Robobi da kayan roba
- Sabulu da kayan kwalliya
- Tumatur da tumaturin leda (ko gwangwani)
- Sayen kuɗin kasar waje/hannun shari/da sauransu
- Masara
- Takin zamani.