An ba da umarnin buɗe iyakokin Najeriya, don a shigo da kayan abinci da sauran kayayyaki

0
229

Babban bankin Najeriya (CBN) ya cire takunkumin da ya ƙaƙaba wajen shigo da wasu kayayyaki tun shekarar 2015.

Sanarwar da babban bankin ya fitar ta bakin Dskta Isa Abdulmumin a shafukansa a ranar Alhamis ya yi bayanin matakin da aka dauka.

Rahoton ya tattaro jerin duka sunayen kayayyaki da yanzu ya halasta ɗan kasuwa ya samu kuɗi domin ya shigo da su.

Kafin yanzu, jaridar ‘The Cable’ ta ce masu buƙatar sayo waɗannan kaya daga ƙasashen ƙetare, suna neman kuɗi ne da tsada a kasuwar canji.

CBN ya yi hakan ne domin yunƙurin tallafawa kamfanonin gida da su ke samar da waɗannan kaya da kuma tsare mutuncin Naira.

KU KUMA KARANTA: Ƙasar Gabon ta sake buɗe iyakokin ƙasar – Sojoji

Ga jerin kayan nan kamar haka:

Kayan da CBN ta cirewa takunkumi

  1. Shinkafa
  2. Siminti
  3. Bota
  4. Kayan man gyaɗa, man ja da sauransu
  5. Nama da kayan nama
  6. Ganye da sauran kayan ganye
  7. Kaji, ƙwai, zabi
  8. Jiragen sama/jiragen yawo
  9. Turaren wutan Indiya
  10. Kifin gwangwani
  11. Naɗaɗɗen rodi
  12. Shafaffen rodi
  13. Kwanon gini
  14. Baro
  15. Kwanon ɗaukar kaya
  16. Akwatin ƙarfe da garwa
  17. Kayan tangaran
  18. Gangunan ƙarfe
  19. Bututun rodi
  20. Wayoyin rodi
  21. Rodi
  22. Ƙarfen waya
  23. Ƙusoshi
  24. Wayar tsaro
  25. Allon katako
  26. Faifen allo
  27. Filai wood
  28. Ƙofofin katako
  29. Kayan jeren gida
  30. Tsinken sakace
  31. Gilas
  32. Kayan girki
  33. Kayan tebura
  34. Tayil
  35. Tufafi
  36. Kayan auduga
  37. Yadi/shaddoji/leshi da saurasu
  38. Robobi da kayan roba
  39. Sabulu da kayan kwalliya
  40. Tumatur da tumaturin leda (ko gwangwani)
  41. Sayen kuɗin kasar waje/hannun shari/da sauransu
  42. Masara
  43. Takin zamani.

Leave a Reply