No menu items!

Sample Page Title

Date:

Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) ta umarci jami’anta da ke faɗin ƙasar su sanya ƙarin matakan tsaro a rumbunanta domin kauce wa masu warwason kayan abinci.

NEMA ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Lahadi da maraice a Abuja.

Kazalika hukumar ta ce rumbun da wasu mutane suka afkawa a Abuja ranar Lahadi inda suka kwashi kayan abinci ba nata ba ne.

Sanarwar ta ce: “Muna yin ƙarin haske da cewa rumbun da aka wawashe ba na NEMA ba ne. Sai dai hukumar tana yin jaje ga waɗanda suka mallaki rumbun.

“A ƙoƙarinmu na hana fuskantar barazana a rumbunan NEMA, darakta janar Mustapha Habib Ahmed ya umarci daraktocin shiyya da shugabannin gudanawa su inganta tsaro a rumbuna da kuma yankunan da ke kusa da su a faɗin Najeriya.”

KU KUMA KARANTA: Rundunar Sojin Najeriya ta gargaɗi masu neman a yi juyin mulki a ƙasar

A baya-bayan nan, wasu ƴan Nijeriya sun riga wawason kayan abinci daga manyan motocin ɗaukar kaya na wasu ƴan kasuwar ƙasar a yayin da ake ta ƙorafi game da tsadar rayuwa.

Lamarin ya yi ƙarami ne tun bayan Shugaba Bola Tinubu ya janye tallafin man fetur, wanda ya ce mutane ƙalilan ne suke amfana da shi, ko da yake wasu ƴan ƙasar na ganin matakin ne ya haddasa ƙarin tsadar rayuwa.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...