An ayyana zaman makoki na kwanaki uku a Masar, saboda jajanta wa ƙasashen Maroko da Libya

0
340

Shugaban Masar Abdel-Fattah al-Sisi a ranar Talata ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku, domin nuna goyon baya da jajanta wa ga ƙasashen Morocco da Libya bayan da ƙasashen biyu suka fuskanci bala’o’i na ibtila’i.

Sisi ya miƙa ta’aziyyarsa da al’ummar Masar ga waɗanda girgizar ƙasar ta shafa a Maroko da guguwar Libiya, kamar yadda fadar shugaban ƙasar Masar ta fitar a cikin wata sanarwa.

Shugaban na Masar ya umarci sojojin ƙasar da su aike da kayan agaji zuwa ƙasashen biyu.

KU KUMA KARANTA: Girgizar ƙasa mai karfin gaske ta kashe mutane 296 a Maroko

Mummunar girgizar ƙasa da ta auku a ƙasar Morocco a daren Juma’a ta yi sanadin mutuwar mutane 2,862 tare da jikkata wasu 2,562, a cewar sabon rahoto daga ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta Morocco.

Guguwar Mediterrenean ta auka wa gabashin ƙasar Libya a ranar Lahadin da ta gabata, lamarin da ya haifar da ambaliya tare da lalata kayayyakin da ke kan hanyarta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 2,300, yayin da wasu 5,000 suka ɓace.

Leave a Reply