An ɗaure matashiya a gidan yari, saboda ta yi duka a Malamar ta

An yanke wa wata ɗaliba ‘yar shekara 15 hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan yarin matasa saboda ta yi wa malamar ta duka a gaban dukkan ɗalibai.

Hotunan faifan bidiyo na matashiyar, wacce ba a bayyana sunanta ba, ya yaɗu a ko’ina a shafukan sada zumunta a watan Janairun 2023, bayan da ta yi wa malamar adabin Burtaniya, Tiwana Turner mummunan duka a makarantar sakandare ta Heritage a Conyers, Georgia.

A cikin faifan bidiyon da aka wallafa a yanar gizo, ana iya ganin ɗalibar tana ihu a fuskar Turner tare da mari wayarta daga hannunta kafin malamar ta yi ƙoƙarin neman taimako yayin da take fita daga cikin aji.

KU KUMA KARANTA: ‘Nakan shafa hoda don ɓoye tabon dukan da mata ta kemim tsawon shekaru 20’ – Ba Ingile

A lokacin da Turner ta hana matashiyar ta rufe mata ƙofa, sai rikici ya ɓarke, yarinyar ta kama gashin malamar ta ja ta ƙasa.

Ta ci gaba da yin shure-shure a ƙasa, yayin da rikici ke gudana a lokacin da ɗalibai ke ciro wayoyinsu don yin rikodin. Harin ya sa malamar ta samu karyewar ƙafa kuma sai da aka fitar da ita daga makaranta a kan shimfiɗa.

A cewar FOX 5 Atlanta, ɗalibar ta amsa laifin da ta aikata, kuma da zarar ta kammala zamanta na shekara guda, za ta shafe shekaru biyar a kan shirin sakin da ake kulawa, in ji mataimakin lauyan gundumar Rockdale.

Watanni uku da faruwar lamarin kuma Turner ta ce har yanzu ba ta iya tafiya da ƙafafunta biyu, tana mai cewa har yanzu tana amfani da sanduna kuma ba ta iya komawa bakin aiki tun daga lokacin. “Ta tafi kawai ta jawo ni ƙasa,” Turner ta tuna harin da aka kai ga FOX5 Atlanta.

Na yi kwana shida a asibiti, rashin lafiyan yana nan duk tsawon kwanaki shida. Ba zan iya zuwa aiki ba, ba zan iya ganin ɗalibai na ba. Ba zan iya yin wani abu da na saba yi ba. Ba zan iya tuƙi ba.


Comments

2 responses to “An ɗaure matashiya a gidan yari, saboda ta yi duka a Malamar ta”

  1. […] KU KUMA KARANTA: An ɗaure matashiya a gidan yari, saboda ta yi duka a Malamar ta […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: An ɗaure matashiya a gidan yari, saboda ta yi duka a Malamar ta […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *