An ƙona zauren majalisar dokokin jihar Ribas, bayan barazanar tsige Gwamna.
Wannan ya zo ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin shirin tsige Gwamna Similanayi Fubara.
Maharan sun samu shiga majalisar dokokin ne a daren ranar Lahadi inda suka ƙona ta.
Rahotanni na nuni da cewa ɗaukin gaggawar da jami’an kashe gobara suka yi ne ya hana gobarar bazuwa a harabar majalisar baki ɗaya.
Ƙoƙarin da aka yi na zantawa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, SP Grace Iringe Koko ya ci tura a lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.
An tsaurara matakan tsaro a harabar ginin yayin da jami’an kashe gobara ke fafatawa don shawo kan gobarar.
KU KUMA KARANTA: Boko Haram sun yi wa tawagar sojoji kwanton ɓauna a Borno, sun kashe soja, sun ƙona fasinjoji da ransu
Sai dai wani rikici ya ɓarke a majalisar dokokin jihar Ribas a ranar Litinin yayin da majalisar ta cire Edison Ehie a matsayin shugaban masu rinjaye.
Edison Ehie babban mai goyon bayan Gwamna Similanayi Fubara ne, sun bayyana cewa ya ba da kunya ga yunƙurin tsige gwamnan.
Da yake sanar da tsige shugaban masu rinjaye a majalisar da ke zamanta a Fatakwal, babban birnin jihar, kakakin majalisar, Martins Amaehwule, ya ce an tsige shi ne saboda rashin halartar zaman majalisar.
Amaehwule yace kimanin ‘yan majalisar 17 ne suka goyi bayan tsige ɗan majalisar.
A halin da ake ciki dai hukumomin tsaro sun mamaye harabar majalisar baki ɗaya.
Wasu da ba a san ko su waye ba sun ƙona zauren Majalisar.
Rahotanni na nuni da cewa hakan ya faru ne da nufin daƙile shirin tsige gwamnan, wanda rahotanni suka ce ya samu saɓani da magabacinsa kuma ministan babban birnin tarayya Abuja (FCT), Nyesom Wike.