An ɗaure wani mutum bisa laifin yin kayan ado da tsabar kuɗin Najeriya

0
972

Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC reshen jihar Kaduna ta gurfanar da wani Ibrahim Musa Dabai a gaban mai shari’a M.N Yunusa na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, jihar Kano, bisa tuhumarsa da laifin yin cuwa-cuwa da kuɗaɗen Najeriya.

Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, (NDLEA), sun kama Mista Ibrahim a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna tare da tsabar kuɗi da ya yi iƙirarin cewa yana yin kayan ado ne don kasuwanci.

Daga nan aka miƙa shi ga hukumar EFCC domin ci gaba da bincike. Wanda aka yankewa hukuncin a yayin gudanar da bincike ya bayyana cewa ya shafe shekaru 25 yana sana’ar canza tsabar kuɗi zuwa kayan ado da suka haɗa da zobe, ‘yan kunne, mundaye da sauransu.

KU KUMA KARANTA: Hukumar EFCC ta kama tsofaffin masu laifi 61 bisa laifin zamba a intanet a Ilori

Laifin ya ƙara da cewa, “Kai Ibrahim Musa Dabai a wani lokaci a cikin Maris, 2023 a Kano, da ke ƙarƙashin ikon babbar kotun tarayya, da son ransa ka yi ta’ammali da kuɗin Najeriya da: tsabar kuɗi da Babban Bankin Najeriya ya bayar a lokacin da ka yi amfani da su don ƙera kayan adon kasuwanci don haka ya aikata laifin da ya saɓawa sashe na 21 (1) na dokar babban bankin Najeriya, 2007”.

Ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi. Lauyan mai shigar da ƙara, N. Salele ya buƙaci kotun da ta hukunta wanda ake tuhuma bisa ga laifin. Mai shari’a Yunusa, ya yanke hukuncin ɗaurin watanni 3 a gidan yari ko kuma tarar Naira 30,000.

Bugu da ƙari, za a mayar da kuɗaɗen da aka lalata zuwa babban bankin Najeriya, CBN domin a lalata su kamar yadda dokar CBN ta 2007 ta tanada.

Leave a Reply