An ɗaure Sarkin Fulani da ‘yan uwansa 2 kan garkuwa da mutane

0
188

Wata babbar kotu da ke zamanta a Ilorin ta yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai ga Sarkin Fulanin Kwara, Usman Adamu, da ɗan uwansa, da wani Gidaddo Idris, bisa samun su da laifin haɗa baki da kuma garkuwa da mutane.

An gurfanar da su ne kuma aka yanke musu hukuncin yin garkuwa da Abubakar Ahmad wani lokaci a shekarar 2022.

An ce waɗanda aka yanke wa hukuncin sun karɓi kuɗin fansa naira miliyan ɗaya kafin su sako wanda aka kama, wanda ya shafe kwanaki 20 a hannunsu.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Najeriya sun ƙuɓutar da mutum 31 da aka yi garkuwa da su a Sokoto

Daraktan shigar da ƙara na jihar Kwara (DPP), Idowu Ayoola, ya gabatar da waɗanda ake ƙara a gaban kotu bisa zargin haɗa baki wajen yin garkuwa da mutane.

A hukuncin da ya yanke, Mai shari’a Adenike Akinpelu, ya ce shaidun da masu gabatar da ƙara suka gabatar sun tabbatar da cewa dukkan waɗanda ake tuhuma uku sun haɗa baki ne don aikata laifin.

Leave a Reply