No menu items!

Sample Page Title

Date:

Wani tsoho da shekara 71 zai yi zaman kaso na tsawon shekaru biyu sakamakon kama shi da hodar ibilis a Kano.

Lauya mai kare tsohon ya ce wannan ne karo na farko da tsohon ya yi aniyar amfani da hodar iblis kuma ya yi nadama.

Sai dai lauya mai gabatar da kara, Aminu Muhammad, yayin gabatar da hujjoji ya tunatar da kotun cewa hodar iblis ba kamar tabar wiwi ba ce, don haka ya kamata a yanke masa  hukunci mai tsanani.

Mai shari’a Muhammad Nasir Yunusa na babbar kotun tarayya da ke jihar Kano, ya yanke wa tsohon tijon mai suna Okey Okosa dan shekara 61 da haihuwa  hukunci zaman gidan yari na shekara biyu.

KU KUMA KARANTA: Ana zargin ‘ma’auratan bogi’ da ɓoye hodar-ibilis a al’aura

An dai kama tsohon ne da laifin mallakar hodar ibilis da ta kai kimanin nauyin gram 2.3.

Wannan ya saba wa sashe na 20 (1) da (c) na dokar kasa da ta tilasta bin doka da oda ta NDLEA.

Okasa ya amsa laifinsa, ya kuma bayyana cewa ya yi nadama.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...