Amurka za ta ɗora alhakin kare lafiyar Bazoum a hannun sojojin Nijar

2
255

Amurka za ta ɗorawa gwamnatin mulkin sojan da ta karɓi mulki a Jamhuriyar Nijar alhakin kare lafiyar zababben shugaban kasar Mohamed Bazoum, da iyalansa, da kuma tsare wasu jami’an gwamnati.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a wata sanarwa da ya fitar ya ce “Amurka ta bi sahun ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) wajen yin ƙira da a maido da tsarin mulki a Nijar.”

A baya-bayan nan ne Amurka ta dakatar da wasu shirye-shiryen ba da taimako ga ƙasar Nijar bayan da sojoji suka hamɓarar da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ta dimokraɗiyya.

KU KUMA KARANTA: Idan sojojin ECOWAS suka yaƙe mu, za mu kashe Bazoum – Jagororin juyin mulkin Nijar

A ranar alhamis ne ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka ta ba da umarnin ƙaddamar da wata rundunar da za ta yi amfani da su wajen yaƙar gwamnatin mulkin sojan da ta karɓi mulki a Nijar a watan Yuli.

Ta ce tana son a maido da mulkin dimokuraɗiyya cikin lumana amma dukkan zaɓukan ciki har da ƙarfi na kan teburin.

A cewar Blinken, Amurka ta yaba da yunƙurin da ECOWAS ta yi na gano duk wani zaɓi na warware rikicin cikin lumana.

Barazanar mamayewa, ko da yake ba a fayyace ta ba, ya ta da tarzoma a ciki da wajen Nijar, mai samar da sinadarin Uranium, wanda har zuwa lokacin juyin mulkin, ya kasance muhimmiyar aminiyar ƙasashen yammacin duniya wajen yaƙi da masu kaifin kishin Islama dake lalata yankin Sahel.

Gwamnatin mulkin sojan da ta karɓe mulki a ranar 26 ga watan Yuli, ta ƙi amincewa da wa’adin da ƙungiyar ta ECOWAS ta ƙayyade a ranar 6 ga watan Agusta, maimakon haka ta rufe sararin samaniyar Nijar tare da sha alwashin kare ƙasar daga duk wani hari da aka kai daga ƙasashen waje.

Ƙungiyar ta yi alƙawarin aiwatar da takunkumi, hana tafiye-tafiye da kuma daskare dukiyoyi a kan waɗanda ke hana komawa kan karagar mulkin Bazoum.

2 COMMENTS

Leave a Reply