Gwamnatin Amurka ta ce a shirye take ta taimaka wa sojojin Najeriya su rage yawan harin bom bisa kuskure da sojojin ƙasar ke kai wa fararen hula.
Amurka ta yi wannan tayin ne bayan harin bom da jirgi mara matuki na sojin Najeriya ya kai wa masu taron Mauludi a Jihar Kaduna, inda ya kashe mutun 90, tare da jikkata wasu 66.
A ranar Alhamis ne Amurka ta sanar da cewa idan Najeriya ta ba ta dama, za ta taimaka wa sojojin ƙasar wasan amfani da fasahar basirar na’uara wajen ƙara karfin sojojin.
Cibiyar kula da makamai ta Amurka ta sanar a Abuja cewa hakan zai kuma taimaka wa sojojin Najeriya ta yadda ba za a same su da karya dokokin duniya a yayin gudanar da aikinsu ba.
KU KUMA KARANTA: Zanga-zanga ta ɓarke a majalisa kan harin Mauludin Kaduna
Jami’in cibiyar Paul Dean, ya kuma yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a harin da jirgin sojin Najeriya ya kashe bisa kuskure a Jihar Kaduna.
Ya shaida wa taron manema labarai cewa ƙasarsa a shirye take ta yaki matsalar kwararar makamai a Najeriya.