Amurka za ta janye dakarunta daga Chadi

0
217

Amurka za ta janye yawancin sojojinta daga Chadi da Nijar yayin da take ƙoƙarin maido da muhimman yarjejeniyoyin da suka shafi rawar da sojojin Amurka za su taka wajen yaƙi da ayyukan ta’addanci, in ji ma’aikatar tsaron Amurka a ranar Alhamis.

Dukkan kasashen Afirka biyu dai na da hannu a yunkurin da sojojin Amurka ke yi na yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a yankin Sahel, amma gwamnatin mulkin Nijar ta kawo karshen wata yarjejeniya a watan da ya gabata, wacce ta bai wa sojojin Amurka damar gudanar da ayyukansu a kasar da ke yammacin Afirka.

A cikin ‘yan kwanakin nan, maƙwabciyar Nijar ɗin wato Chadi ita ma ta nuna shakku kan ko yarjejeniyar da aka cimma ta shafi sojojin Amurka da ke aiki a can.

Sakataren yada labarai na Pentagon, Manjo Janar Pat Ryder, ya fada a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai cewa, Amurka za ta mayar da kusan kusan dakaru 100 da ta girke a kasar Chadi.

KU KUMA KARANTA: Ƴan gudun hijirar Sudan da ke Chadi na fuskantar tsananin rayuwa shekara guda da soma yaƙi

Wani jami’in Amurka da ya nemi a sakaya sunansa ya ce wasu gomman dakaru na musamman da ke kasar Chadi a matsayin masu tsara tsare-tsare da masu ba da shawara za su koma Jamus a yanzu.

A farkon wannan watan ne babban hafsan sojin saman Chadi ya umarci Amurka da ta dakatar da ayyukan da ake yi a wani sansanin sojin sama da ke kusa da N’Djamena babban birnin kasar, kamar yadda wata wasika da aka aike wa gwamnatin riƙon ƙwarya da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.

In the letter dated April 4 to Chad’s minister of armed forces, Air Force Chief of Staff Idriss Amine Ahmed said he had told the U.S. defence attache to halt U.S. activities at Adji Kossei Air Base after “Americans” had failed to provide documents justifying their presence there.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan wata 4 ga Afrilu Ministan Tsaron kasar Chadi, babban hafsan sojin sama Idriss Amine Ahmed ya ce ya shaida wa jami’an tsaron Amurka da su dakatar da ayyukan Amurka a sansanin jiragen sama na Adji Kossei bayan “Amurkawa” sun kasa samar da wasu takardu da ke tabbatar da kasancewarsu a can.

“Yayin da ake ci gaba da tattaunawa da jami’an kasar Chadi, a halin yanzu AFRICOM na shirin mayar da wasu sojojin Amurka daga kasar Chadi, wadanda tuni aka shirya barin wasu sassansu. Wannan wani mataki ne na wucin gadi a zaman wani bangare na ci gaba da nazari kan hadin gwiwarmu na tsaro, wanda zai ci gaba da kasancewa bayan zaben shugaban kasar Chadi a ranar 6 ga watan Mayu,” in ji Ryder.

A jamhuriyar Nijar, yawancin ma’aikatan Amurka 1,000 da aka tura can su ma ana sa ran za su tashi, in ji Ryder.

Ana sa ran jami’an Amurka da na Nijar za su gana a ranar Alhamis a Yamai babban birnin Nijar, domin fara tattaunawa kan janye sojojin Amurka cikin tsari da sanin ya kamata,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin ranar Laraba.

Ana sa ran taruka za su biyo baya tsakanin manyan jami’an Pentagon da Nijar a mako mai zuwa “don daidaita tsarin janyewar cikin gaskiya da mutunta juna,” in ji Ryder.

Leave a Reply