Amurka ta tura sojoji dubu biyu, don shirin ko-ta-kwana kan rikicin Gaza da Isra’ila

0
361

Rundunar sojin Amurka ta tura sojoji 2,000 a shirin ko-ta-kwana a daidai lokacin da ake ƙara samun rikici tsakanin Isra’ila da Hamas.

Hedikwatar tsaron Amurka ta Pentagon ce ta tabbatar da hakan a ranar Talata.

Kafofin watsa labaran Amurka sun bayyana cewa dakarun ko sun je can za su bayar da tallafin kiwon lafiya ne da kuma kawar da bama-bamai.

Wannan matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake sa ran Shugaban Amurka Joe Biden zai tafi Isra’ila a ranar Laraba domin nuna goyon bayan Amurka ga babbar ƙawar ƙasar wato Isra’ila.

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi gargaɗi kan cewa matsalar ƙarancin abinci na ƙara ƙaruwa a Zirin Gaza da Isra’ila ta yi wa ƙawanya.

Shirin na WFP ya bayyana cewa a halin yanzu abincin kwanaki huɗu zuwa biyar ya rage a shaguna.

KU KUMA KARANTA: Iran ta gargaɗi Isra’ila kan ci gaba da kai hari kan Falasɗinawa

WFP ɗin ya ce kayayyaki na ƙara raguwa a manyan ɗakunan ajiye kayayyaki da ke cikin Falasɗinu amma lamarin ya fi ƙamari a shaguna.

Shirin na WFP ya ce cikin gidajen burodi 23 da ya bai wa kwangila biyar ne kacal ke iya aiki.

Sarki Abdullah II na Jordan ya gana da Shugaban Gwamnatin Jamus OIaf Scholz a Berlin inda ya ce ƙasarsa da kuma ƙasar Masar ba za su amince su karɓi duk wani ɗan gudun hijira na Falasɗinawa ba.

“Dole a shawo kan wannan lamari a cikin Gaza da Gaɓar Yammacin Kogin Jordan,” in ji shi. “Kuma bai kamata wasu su ɗauki alhakin wannan batu ba.”

Kazalika Abdullah ya ce ya kamata a ɗauki dukkan matakan da suka dace wajen ganin an kauce wa ta’azzarar yaƙi tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa.

“Gaba ɗaya yankin yana fuskantar bala’i,” in ji Abdullah. “Wannan sabon rikicin zai iya kai wa ga wargajewarmu.”

Leave a Reply