Amurka ta soke tallafin da take bai wa ƙasar Gabon

0
188

Janar Brice Oligui Nguema, wanda daɗaɗɗen na hannun-daman Bongo ne, ya jagoranci yi masa juyin mulki a watan Agusta.

Amurka ta ce ta daina bayar da tallafi ga Gabon sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi ranar 30 ga watan Agustan da ya gabata.

Wata sanarwa da kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen ƙasar Matthew Miller ya fitar ranar Litinin ta ce “za mu ci gaba da bayar da tallafi ne idan muka ga gwamnatin riƙon ƙwarya ta ɗauki ƙwararan matakai na komawa kan turbar mulkin dimokuraɗiyya.”

Amurka, wadda da ma ta dakatar da bai wa ƙasar wasu tallafi, ta ƙara da cewa a hukumance yanzu ta tabbatar an yi juyin mulki a Gabon abin da ke nufin ba za a ci gaba da bai wa ƙasar taimakon jinƙai ba kamar yadda dokokin Amurka suka tanada.

Sojojin Gabon sun kifar da gwamnatin daɗaɗɗen shugaban ƙasa Ali Bongo Ondimba a daidai lokacin da hukumar zaɓen ƙasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara karo na uku a zaɓen da aka gudanar wanda ke cike da zargin tafka maguɗi.

KU KUMA KARANTA: Amurka ta soke tallafin dala miliyan 442 da take ba wa Nijar

An ayyana Janar Brice Oligui Nguema a matsayin shugaban riƙon ƙwarya yayin da aka naɗa Raymond Ndong Sima, fitaccen mai adawa da Bongo, a matsayin firaiminista.

Ndong Sim ya roƙi ƙasashen Yamma ka da su kwatanta juyin mulkin da aka yi a Gabon da waɗanda aka yi a wasu ƙasashen Afirka, yana mai cewa sojoji sun kifar da gwamnatin ƙasar ne domin hana tarzoma da shawo kan matsalar cin-hanci da rashawa.

Tuni dai aka ɗaure Sylvia Bongo Ondimba Valentin, matar tsohon shugaban ƙasar, kan zarge-zargen almubazzaranci da kuɗaɗen al’umma.

Leave a Reply