Amurka ta nemi China ta yi wa Iran magana kan hare-haren Houthi

0
128

Daga Ibraheem El-Tafseer

Jami’an Amurka sun ce sun buƙaci China ta nemi Iran ta tsawatar kan hare-haren mayaƙan Houthi da suke kai wa jiragen kasuwancin ƙasashen duniya a ruwan maliya.

Wasu jami’ai da suka nemi a sakaya sunayensu, sun shaida wa Reuters cewa fadar White House ce ta tura wannan buƙata ta ofishin mai bayar da shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan yayin tattaunawarsa da Ministan Harkokin Wajen China Wang Yi.

An yi wannan tattaunawa ne a ranar Juma’a da Asabar a Bangkok da zummar rage rashin jituwar da ke tsakanin ƙasashen biyu kan lamarin Taiwan, gabanin ganawar da shugabanin ƙasashen biyu za su yi a nan gaba.

Leave a Reply