Amurka ta kai harin ramuwar gayya a Syria da Iraki

0
139

Rundunar sojin Amurka ta ce dakarunta sun ƙaddamar da jerin hare-hare ta sama a wasu yankuna na Syria da Iraki domin yin ramuwar gayya kan kisan sojojinsu uku da aka yi a wani sansanin sojin Amurka da ke kan iyakar Jordan da Syria.

Dakarun sojojin Amurka sun kai hare-hare kan runduna ta musamman ta Revolutionary Guards ta Ira da kuma ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke da Tehran inda hare-haren suka sauka a fiye da yankuna 85 a Iraki da Syria, a cewar rundunar ranar Juma’a.

“An kai hare-haren na sama ne da makamai fiye da 125 da ke iya sauka a wurin da aka cilla su ba tare da kuskure ba,” a cewar Rundunar da ke bayar da umarni ta sojojin Amurka a wani sako da ta wallafa a soshiyal midiya.

KU KUMA KARANTA: Amurka ta sake nanata ƙudurinta na tsayawa tsayin daka a fannin tattalin arziƙi da kasuwanci a ƙasashen Afirka.

Ta ƙara da cewa an kai hare-haren ne a cibiyoyin bayar da umarnin soji da na leƙen asiri da rokoki da makamai masu linzami da wuraren ajiye jirage marasa matuka na masu tayar da kayar baya da kuma dakarun tsaron Iran “waɗanda suke taimaka wa wurin kai hare-hare kan Amurka da kawayenta.”

Shugaba Joe Biden ya jaddada cewa Amurka za ta ƙara ƙaimi wurin mayar da martani. “Mun soma mayar da martani yau kuma za mu ƙara ƙaimi wurin yin hakan a wurare da lokutan da muka sanya wa ido,” in ji Biden.

“Duk da yake Amurka ba ta tsokanar faɗa a Gabas ta Tsakia da wasu yankuna, ina so na bayyana ƙarara cewa duk wanda ya ce mana kule, za mu masa cas,” a cewar shugaban Amurka.

Jami’an gwamnatin Iraki sun yi tir da waɗannan hare-hare a kan iyakokinsu, suna masu cewa hakan ya ƙeta alfarmarsu ta kasancewa kasa mai cin gashin kanta sannan za su nuna fushinsu mai girma.

Janar Yehia Rasool, kakakin Firaiminista Mohamed Shia al Sudani, ya yi gargadi cewa harin da aka kai a yammacin Iraki, kusa da kan iyaka da Syria, zai iya jefa yankin cikin hatsari.

Leave a Reply