Amurka ta harbo makami mai linzami da jirage marasa matuƙa da Houtji suka harba

0
167

Wani jirgin ruwa na Amurka ya harbo jirage marasa matuka da makami mai linzami da ‘yan Houthi na Yaman suka harba a cikin Bahar Maliya, in ji jami’an Amurka, a daidai lokacin da sojojin ruwan Indiya suka fitar da hotunansu na yadda suka kashe gobarar da ta kama a cikin wani jirgin ruwan kwantena da ‘yan Houthi suka fara kai wa hari.

Harin na Houthi ya hada da jirage marasa matuka masu dauke da bama-bamai da makami mai linzami guda daya na kakkaɓo jiragen ruwa, in ji rundunar sojin Amurka.

KU KUMA KARANTA: Rasha ta yi atisayen harba makamin nukiliya

Daga baya Amurka ta kai wani hari ta sama, inda ta lalata makami mai linzami guda uku da jiragen ruwa marasa matuka guda uku masu dauke da bama-bamai, in ji rundunar ta tsakiya.

Leave a Reply