Amurka ta ci tarar kamfanin ƙera motocin lantarki na Tesla dala miliyan ɗaya da rabi

0
123

Wani Alƙali a jihar California ta Amurka ya bayar da umarni ga kamfanin Tesla ya biya diyyar dala miliyan 1.5 kan zargin sakaci wurin zubar da shara mai hatsari a wuraren da kamfanin ke ƙera motocinsa.

Ƙorafin wanda aka shigar a yankin San Joaquin, an yi zargin cewa an zubar da sharar mai hatsari ga bil adama da kuma karya dokokin zubar da shara, kamar yadda wasu jerin sanarwa masu yawa waɗanda suka fito daga lauyoyi 25 na gundumar a California waɗanda ke da alaka da shari’ar wadda aka yi a ranar Juma’a suka nuna.

Tesla dai ba ta mayar da martani nan take ba kan saƙon da kamfanin dillancin labarai na AP ya aike mata.

Sai dai sanarwar da kotun ta fitar ta tabbatar da cewa kamfanin na Tesla ya bayar da haɗin kai wurin gudanar da bincike kuma ya ɗauki matakai domin ganin cewa an gudanar da abubuwa bisa tsari bayan masu shigar da ƙara sun jawo hankalinsa.

KU KUMA KARANTA: Kotu ta ci tarar Gwamnan Kano N25m kan zargin Alhassan Doguwa da kisa

“Motoci masu amfani da lantarki suna taimaka wa muhalli, sai dai yana da kyau a san cewa samar da su da kuma kula da su na samar da shara da yawa,” kamar yadda lauyan na San Joaquin ya bayyana.

Tesla tana da wuraren gyaran motoci nata na kanta kimanin 57 da kuma wuraren makamashi na hasken rana a California, tare da ƙera motoci masu lantarki a San Francisco.

Leave a Reply