No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaba Joe Biden ya ce Isra’ila za ta amince ta dakatar da yaƙin da take yi a zirin Gaza a lokacin azumin watan Ramadana mai zuwa idan har aka cimma matsaya na sako wasu daga cikin mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

Masu shiga tsakani daga ƙasashen Amurka da Masar da kuma Qatar na aiki kan wani shiri na yarjejeniya wadda a ƙarƙashinta ake sa Hamas za ta saki fursunonin yaƙi da dama da ta yi garkuwa da su, inda ita kuma Isra’ila ta sako fursunonin Falasɗinawa da kuma tsagaita wuta tsawon makonni shida.

A lokacin tsagaita wutar ta wucin-gadi, za a ci gaba da tattaunawa kan sakin sauran waɗanda aka yi garkuwa da su.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...