Amurka ta buƙaci MƊD ta goyi bayan tsagaita wuta na wucin gadi a Gaza don ƴantar da fursunoni

0
172

Amurka ta sake yin gyaran fuska a cikin wani daftarin ƙudiri na Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya don goyan bayan “tsagaita wuta nan da nan na kusan makonni shida a Gaza tare da sakin dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su,” a cewar labarin da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.

Bita ta uku ta rubutun – wacce da farko Amurka ta gabatar makonni biyu da suka gabata – yanzu tana nuna kaifafan maganganun da Mataimakiyar Shugaban Ƙasa Kamala Harris ta yi.

Daftarin farko na Amurka ya nuna goyon baya ga “tsagaita wuta na wucin gadi” a cikin kisan gillar da Isra’ila ta yi a yankin Falasɗinawa da ta yi wa ƙawanya.

KU KUMA KARANTA: Adadin waɗanda suka mutu a Gaza ya haura 30,534 yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare

Amurka na son duk wani goyon bayan kwamitin sulhu na tsagaita wuta ya kasance yana da alaka da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

Leave a Reply