Amurka ta bai wa Ukraine harsashi miliyan ɗaya da ta ƙwace daga Iran

0
221

Rundunar sojojin Amurka ta ce ta aika da harsashi kimanin miliyan da dubu ɗari ɗaya zuwa Ukraine, waɗanda ta ƙwace daga Iran a bara.

Bataliyar Amurka da ke sanya idanu kan ayyukan Gabas ta Tsakiya ce ta bayyana hakan, an ƙwace harsashin ne daga wani jirgin ruwa da aka kama yana nufar Yemen a watan Disamba.

Ukraine wadda ke ƙawance da ƙasashen yamma, ta yi kukan cewa a ‘yan kwanakin nan tana fama a yaƙin da take yin da rashin harsashi.

A ranar Litinin ne Centcom ta ce ta aika hasashen da ta ƙwace daga Iran zuwa Ukraine.

KU KUMA KARANTA: Harin makami mai linzami a Yukren ya kashe mutane 16

Dakarun rundunar sojin ruwan Amurka ne suka ƙwace harsashan daga wani jirgi da ba a gano na wacce ƙasa ba ne mai suna MARWAN 1 a ranar 9 ga watan Disamba, in ji ta.

A watan Yuli Amurka ta ayyana mallakar harsashen ƙarƙashin dokar ‘yan sanda ta ƙwace abubuwan da ba su dace ba, wacce ke ƙwace kayayyakin mutanen da aka samu da aikata manyan laifuka.

A wannan lamari, an yi iƙirarin cewa kayan mallakin rundunar juyin juya hali ne ta Iran, ƙarƙashin wata tawaga da aka ɗorawa aikin lura da killace kayyakin gwamnatin ƙasar.

Wata sanarwa da rundunar sojin Amurka ta fitar ta ce Amurka “na aiki tuƙuru tare da abokanta da ƙawayenta domin daƙile duk wani taimakon da Iran ke aikewa a yankin ta hanyar da ta dace”.

Iran na goyon bayan ‘yan tawayen Houthi a yaƙin da ake yi a Yemen, sai dai kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya haramta aike wa da ƙungiyar makamai ƙarƙashin wata doka ta 2015.

An fara yaƙin basasa a Yemen a 2014, lokacin da Houthi ta karɓe iko da Sanaa babban ƙasar ta kuma tuɓe gwamnatin ƙasar.

Hamɓararriyar gwamnatin dai ita ce ƙasashen duniya suka sani a Yemen, kuma tana samun goyon bayan tawagar ƙawancen sojin ƙasashe da Saudiyya ke jagoranta a yankin kazalika da goyon bayan Amurka da na Burtaniya.

Tun a tsakiyar bara, ake ta zargin Iran da kai wa Rasha makamai, musamman jirage maras matuƙa, domin amfani da su a yaƙin da take da Ukraine.

A ranar Litinin, a wani mataki kan yadda ƙasashen Yamma za su ci gaba da bai wa Ukraine hasashi da ya gudana a Warsaw, Adm Rob Bauer, shugaban kwamitin sojojin ƙungiyar tsaro ta Nato ya ce “duk abin da ake akan idonsu ake yi”.

Yace rashin zuba jari na gwamman shekaru na nufin, ko a farkon yaƙin, rumbur ajiyar hasasai na ƙasashen ƙungiyar tsaro ta Neto ya haura rabi ko ma ya ƙare.

Ya ƙara da cewa “akwai buƙatar masana’antu da gwamnatoci su ƙara yawan hasasan da suke samarwa cikin sauri”.

Leave a Reply