Amurka na son ci gaba da ƙawance da Nijar kan tsaro da haɗin kai

0
150

Amurka ta yi niyyar ci gaba da ƙawance da Jamhuriyar Nijar game da harkokin tsaro da ci-gaba muddin sojojin ƙasar suka ɗauki matakin dawo da dimokuraɗiyya, a cewar wata jami’ar diflomasiyyar ƙasar.

Molly Phee, Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka kan Afirka, ta bayyana haka ne ranar Laraba a Yamai bayan ta gana da shugabannin sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a watan Yuli.

Phee ta ce ta fayyace wa shugabannin sojojin da ake ƙira CNSP “ƙarara” cewa “muna son sake zama ƙawaye na gari da Nijar, amma dole ne su ma CNSP su zama nagartattun ƙawaye ga Amurka.”

“A tattaunawar da muka yi, na tabbatar musu cewa Amurka na shirin dawo da hulɗa ta tsaro da ci-gaba daki-daki, amma ya kamata su ma CNSP su ɗauki mataki.”

KU KUMA KARANTA: Nijar, Mali da Burkina Faso za su samar da takardar kuɗin bai-ɗaya – Tiani

Amurka ta sanar da hakan ne kwanaki kaɗan bayan Nijar da Rasha sun sanya hannu kan yarjejeniyar ƙarfafa hulɗa a fannin tsaro yayin ziyarar da Mataimakin Ministan Tsaron ƙasar Yunus-bek Yevkurov ya kai Yamai.

Kazalika Amurka ta yi wannan kalami ne bayan da a kwanakin baya sojojin Nijar suka soke yarjejeniyar tsaro guda biyu da Tarayyar Turai.

Masu sharhi sun ce Amurka da sauran ƙasashen Yamma na cike da fargaba game da ƙawancen da Rasha ta ƙulla da Nijar, matakin da ka iya zama barazana a gare su.

Rasha na ci gaba da ɗaukaka dangantakan tsaro tsakaninta da ƙasashen Yammacin Afirka, ciki har da Mali da Burkina Faso.

Leave a Reply