A ranar Laraba ne Amurka da Rasha za su gabatar da muhawara a shari’ar da ake yi a Kotun Ƙolin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke nazarin halaccin mamayar da Isra’ila ke yi a yankin Falasɗinu.
Fiye da ƙasashe 50 ne za su gabatar da muhawara har zuwa ranar 26 ga watan Fabrairu. An kuma shirya Masar da Faransa su yi magana ranar Laraba.
KU KUMA KARANTA: Shugaban ‘yan adawa a Rasha, ya mutu a gidan yari
A ranar Talata, ƙasashe 10 ciki har da Afirka ta Kudu, sun yi kakkausar suka ga yadda Isra’ila ke gudanar da ayyukanta a yankunan da ta mamaye, inda da dama suka buƙaci kotun da ta ayyana mamayar a matsayin haramtacciya.