No menu items!

Sample Page Title

Date:

Amnesty International ta koka kan yadda wasu Gwamnatoci ke kama ‘yan gwagwarmaya

Daga Jameel Lawan Yakasai

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International ta koka kan yadda ake ƙara yawaitar kama ‘yan gwagwarmaya da ke sukar muradan gwamnatoci a ƙasar nan.

Ƙungiyar ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta nuna damuwa kan yadda ake amfani da wasu tsare-tsare wajen tsoratarwa da take ’yancin faɗar albarkacin baki.

Sanarwar ta ce daga cikin waɗanda abin ya rutsa da su a baya-bayan nan akwai Hassan Kangiwa daga Jihar Kebbi, Hussaini Bello Nakura daga Jihar Adamawa da kuma Daure David daga Jihar Bauchi.

KU KUMA KARANTA: Matsalar tsaro na ƙara taɓarɓarewa a Najeriya – Amnesty

Ƙungiyar ta ce gwamnati na nuna rashin juriya ga waɗanda ke bayyana ra’ayoyinsu ta kafafen sada zumunta ko kuma a bainar jama’a, abin da ta kira take haƙƙin bil’adama.

Ta kuma bayyana cewa kama mutum saboda sukar gwamnati ko jami’anta ba shi da tushe balle makama.

Amnesty International ta yi kira ga hukumomi su daina kama ’yan ƙasa saboda sukar shugabanni,

Maimakon hakan su mayar da hankali wajen magance matsalolin da suka shafi cin hanci, nuna son kai da halin ƙuncin tattalin arziƙi, waɗanda ke tilasta jamaʼa su koka.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...