Amfanin manhajar XENDER a wayoyin hannu

Daga Ibraheem El-Tafseer

Xender manhaja ce da muka fi sani wajen yin aika wa da karɓar saƙo wato ‘transfer’ na ‘files’ (videos, audios, photos, applications da sauransu) daga wata wayar zuwa wata waya daban. A tsakanin Android da Android, ko Android da iPhone, ko tsakanin Android da KaiOS, ko kuma tsakanin waya da computer.

Akwai kuma wasu muhimman aiyuka da za mu iya yi da Xender wanɗanda suka haɗa da:

  1. Sauƙe status na WhatsApp
  2. Sauƙe ‘video’ daga Facebook, Twitter da Instagram
  3. Converting na ‘video’ zuwa ‘Audio’
  4. Mayar da kayan (files) na tsohuwar waya zuwa sabuwar waya (cloning)

Yadda Ake Sauƙe Status (Video ko Photo) daga WhatsApp

Kafin ka sauƙe ‘status’ na WhatsApp ta hanyar amfani da Xender, sai ka buɗe (status viewing) ta WhatsApp da farko tukunna, sai ka shiga cikin Xender, ka duba can ƙasa, za ka ga ‘social’, sai ka shiga ‘social’. Duk ‘status’ ɗin da ka buɗe za su fito a nan, sai ka zaɓa, ka yi ‘saving.’

Yadda Ake Sauƙe Video Daga Facebook, Twitter Da Instagram

Idan kana buƙatar sauƙe (downloading) na wani ‘video’ daga Facebook, Twitter ko Instagram ta hanyar amfani da Xender ga matakan da zaka bi:

KU KUMA KARANTA: Yadda ake tantance (Verifying) Facebook account da Facebook Page

  • Za ka yi ‘copy’ na link ɗin wannan videon.
  • Sai ka buɗe Xender, ka shiga wannan wajen na ‘SOCIAL’
  • Sai ka shiga wajen da aka rubuta ‘PASTE AND DOWNLOAD’, sai ka buɗe, ka yi ‘paste’ na wancan link da ka yi copied ɗin. Wato ka danne ya tsanka a wajen, za ka ga link ɗin ya sauka.
  • Zai yi ‘analyzing’ na link ɗin na lokaci kaɗan, sai kuma ya fara sauka (downloading).

YADDA AKE MAYAR DA VIDEO ZUWA AUDIO (CONVERTING) A XENDER

Ana iya amfani da Xender wajen mayar da video na kallo, zuwa audio na saurare. Wato ‘converting’ na ‘video’ ya koma ‘audio’ ta waɗannan matakan:

  • Ka shiga cikin ‘Xender’
  • Ka duba daga can ƙasa, za ka ga wani waje ‘bottom’ an rubuta ‘ToMp3’, sai ka shiga ciki.
  • A ciki, zai baka zaɓi guda biyu. Na farko, ToMp3, na biyu kuma LOCAL. Za ka iya shiga ta kowannensu, don nemo ko zaɓar videon da kake son mayar wa Mp3 ɗin (audio).

MAYAR DA KAYAN (FILES) NA TSOHUWAR WAYARKA ZUWA SABUWAR WAYA

Idan ka canza wayarka, wato ka sayi sabuwar waya, kuma kana so ka ka kwashe abubuwan ka na kan tsohuwar wayar ta ka, to ana amfani da Xender cikin sauƙi wajen kwashe su.
Xender tana da tsarin CLONE, tsari ne da zai ba ka damar ‘transfer’ na ‘files’, applications, contacts da sauransu, daga wata wayar zuwa wata wayar.

Wannan tsarin na CLONE zai ba ka damar ɗebe kayan tsohuwar wayarka, zuwa sabuwa ba tare da ka rasa komai ba, ciki har da ‘messages’ da ‘call history’.

Yadda za ka yi amfani da wannan tsarin na XENDER CLONE shi ne:

  • Ka duba cikin Xender da kyau, daga can sama (ɓangaren dama) akwai wasu ɗigo guda uku, icons ≡, sai ka shige shi.
  • A menu ɗin, ka duba na ƙarshe, shi ne ‘phone copy’, sai ka shige shi.
  • Sai ka zaɓa a cikin wayoyin biyu, ɗaya NEW (wacce za a turawa), ɗaya kuma OLD (wacce za ta tura ɗin).

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *